Abdullahi Adamu da Kwamitin NWC Zasu Gabatar da Ahmad Lawan ga Buhari – Sanata Orji Kalu

Abuja – Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a APC, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa shugaban jam’iyya, Abdullahi Adamu, da kwamitin gudanarwa NWC zasu gabatar da Lawan ga Buhari.

Punch ta rawaito cewa Adamu da sauran yan kwamitinsa na NWC zasu kai wa Buhari sunan Ahmad Lawan ne domin ya goya masa baya a matsayin ɗan takarar maslaha.

Rahoton da ya karaɗe kafafen watsa labarai ya nuna cewa Adamu ya zaɓi shugaban majalisar dattawa a matsayin ɗan takarar sulhu yayin da zaɓen fidda gwani zai gudana yau Talata.

Bayan haka ne, Mambobin NWC da kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, suka fito suka shaida wa duniya cewa ba su da hannu a zaɓen ɗan takarar maslaha.

Sun jaddada cewa dukkan yan takara zasu haɗu a waktin zaɓe yayin da Deleget zasu raba gardama kan wanda zai karbi tutar jam’iyya a babban zaɓen dake tafe.

Kalu ya taya Sanata Ahmad Lawan Murna

A wata sanarwa da ya ratfaɓa wa hannu. da kansa, Sanata Kalu ya taya Ahmad Lawan murna tare da cewa za’a kai wa Buhari sunansa domin mara masa baya.

Ya ce:

“Bayan dogon nazari kan yan takarar mu da suka cancanta, Sanata Abdullahi Adamu, ya yanke cewa Ahmad Lawan ne ya dacewa ya zama ɗan takarar APC a zaben shugaban ƙasa 2023.”

‘”Shugaban jam’iyya da kwamitin gudanarwa NWC zasu gabatar da sunan Lawan ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, domin ya mara masa baya.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here