An Gurfanar da Direban da ya Daba wa Fasinja wuƙa Kan N100

An gurfanar da wani direban motar haya a gaban kotun Majistare a Kaduna kan zarginsa da caka wa fasinja wuƙa.

Mai gabatar da kara a kotu, Sufeta Leo Chidi ya ce direban aka ake zargi ya daba wa fasinjan wukan ne kan N100 da suke rikici a kai.

Direban da aka yi ƙarar a kotu, mazaunin Gonin-Gora a Kaduna ya musanta zargin da aka masa kuma Alkali ya bada belinsa kan N200,000 ya dage cigaba da sharia.

Kaduna – An gurfanar da wani direban mota, Silas Vincent, dan shekara 38 a gaban kotun Majistare da ke Kaduna kan zarginsa da daɓa wa fasinjansa wuka yayin musu kan kudin mota.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN ta rahoto cewa yan sanda sun gurfanar da mutumin mazaunin Gonin-Gora a Kaduna kan laifin kai hari da yin mummunan rauni.

Mai gabatar da kara, Sufeta Chidi Leo, ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a Stadium Round About, Ahmadu Bello Way Kaduna a ranar 28 ga watan Mayu.

A cewar Leo, rikici ya barke tsakanin wanda aka yi ƙarar da wani Emmanuel Isaac kan kudin mota N100. Mai gabatar da karar ya ce yayin fadar, wanda aka yi ƙarar ya ciro wuka daga aljihunsa ya caka wa wanda ya yi ƙarar a kafadarsa da bayansa.

Leo ya ƙara da cewa an garzaya da wanda ya yi ƙarar zuwa wani asibiti da ke kusa inda aka yi masa magani.

Mai gabatar da ƙarar ya ce laifin ya saba da sashi na 173 da 284 na Penal Code na Jihar Kaduna ta shekarar 2017.

Martanin wanda aka yi ƙarar

Bayan karanto masa tuhumar, wanda aka yi ƙarar ya musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel ya bada belin wanda ake zargin kan kudi N200,000 tare da mutum biyu wanda za su tsaya masa. Ya dage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Yuni kamar yadda NAN ta rahoto.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here