Shugaban NITDA ya Halarci Taro Kan Tattalin Arziki da Ministan Sadarwa Bisa Jagorancin Shugaba Buhari
Read Also:
Mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), a ya yin halartar taron tattalin arziƙi na ƙasar Nageriya da ƙasar Spain tare da mai girma ministan sadarwa da tattalin arziƙin fasahar zamani, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS FIIM) a bisa jagorancin mai girma shugaban ƙasar tarayyar Nageriya, Malam Muhammadu Buhari (GCFR).
Taron wanda aka yi wa take da: “Nigeria-Spain Business & Trade Forum”, ya gudana ne a birnin Madrid na ƙasar ta Spain a wannan rana inda aka tattauna kan yadda za a samar da haɗaka a tsakanin ƙasashen biyu wajen ganin masu zuba jari kan harkokin fasahar zamani da nau’in kasuwanci sun shigo Nageriya sun zuba jari domin samarwa ƙasar ƙarin cigaban arziƙi.