Tukunyar Gas ta yi Sanadiyyar Jikkata Mutane 20, da ƙona Shaguna a Kano

An samu fashewa a shagon sayar da gas ɗin girki a wata unguwa da ke cikin garin Kano, lamarin da ya jikkata mutum 20 da ƙona shaguna da dama.

Wannan na zuwa ne makwanni bayan samun shigen wannan fashewar a titin Aba ta kasuwar Sabon Gari a Kano, inda mutum 9 da suka mutu baya ga wadanda suka jikkata.

Ko da yake a wannan lokacin an yi ta samun bayanai masu cin karo da juna, rundunar ‘yan sanda na cewa tukunyar gas ce, ganau kuma na cewa bam ne.

Rahotanni dai na cewa iftila’in na wannan lokaci ya faru ne a unguwar Sheka, Karshen-Kwalta.

Kuma babu bayanai da aka samu na mutuwa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here