Abinda NLC Keyi Tamkar ‘Yan Bindiga ne, Masu Garkuwa da Mutane da Suka Addabi Al’umma – Gwamna El-Rufa’i
Gwamna Nasir El-Rufai ya sha alwashin sallamar dukkan ma’aikatan da suka shiga zanga-zangar kungiyar kwadago a jahar.
An kulle gidajen mai, bankuna, tashohiin jirgin sama da kasa, dss.
El-Rufa’i ya sallami malaman jinya, malaman jami’a da suka shiga yajin aikin.
Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya siffanta shugabannin kungiyar kwadago, NLC, da suka shirya yajin aiki da zanga-zanga kan sallamar ma’aikata a jahar matsayin yan bindiga.
Read Also:
Ya lashi takobin hukuntasu, inda ya tuhumcesu da lalata dukiyoyin gwamnati da kuma tayar da tarzoma.
A cewar El-Rufa’i, basu da banbanci da yan bindiga masu garkuwa da mutane da suka addabi al’ummar jahar.
Hakazalika ya bada umurnin sallamar Malamn jami’ar Kaduna KASU da suka shiga yajin aikin na kwanaki 5.
Mai magana da yawun El-Rufa’i, Muyiwa Adekeye, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Litinin a Tuwita.
Yace:
“Gwamnatin Kaduna na ganin wannan abin da NLC keyi tamkar yan bindiga masu garkuwa da mutane da suka addabi al’umma.”
“Yan bindiga na amfani da makamai, amma NLC na amfani da nasu wanda manufarsu guda: hana mutane yanci, dakile tattalin arziki, da kuma lalata dukiyoyin al’ummar Kaduna.”