Majalisar Dattijai ta Nemi JAMB da ta Soke Amfani da NIN Wajen yin Rijista

 

Majalisar dattijai ta umarci JAMB da ma’aikatar ilima su soke wajabcin amfani da NIN wajen yin rijista.

Majalisar tace kamata yayi hukumar NIMC ta nemo hanya mafi sauƙi da zata ba ɗaliban sakandire damar mallakar NIN a makarantunsu.

A wannan shekarar ne dai JAMB ta sanar da cewa ya zama wajibi kowane ɗalibi ya mallaki NIN idan yana son zana jarabawarta.

A zaman majalisa na Talata, yan majalisar dattijai sun umarci hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB da ma’aikatar ilimi su soke wajabcin amfani da lambar NIN ko su ƙara lokacin yin rijista.

Majalisar ta umarce su da su sake duba shirin amfani da NIN ɗin a lokacin yin rijista, kamar yadda BBC ta ruwaito.

A wannan shekarar ne, hukumar JAMB ta maida amfani da NIN wajibi ga duk ɗalibin dake son zana jarabawar shiga manyan makarantu.

Sai dai a rahoton premium times, yan majalisar sun umarci JAMB da ta ƙara wa’adin yin rijista ko kuma ta soke amfani da NIN. Wannan na ƙunshe ne a wani kudiri da Sanata Ifeanyi Ubah daga Jahar Anambra ya gabatar a gaban majalisar a zamanta na yau.

Kudirin ya ƙunshi umarni ga ma’aikatar ilimi, hukumar samar da katin ɗan ƙasa (NIMC) da su nemo wata hanya da zata sauƙaƙa wa ɗalibai wajen samun lambar NIN a makarantunsu. Kudirin ya kuma bayyana cewa dokar da JAMB tayi cewa wajibi ne kowane ɗalibi dake son zana jarabawa yayi amfani da lambar NIN ya saka ɗaliban cikin wahala.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here