NLC ta ba Gwamnoni Wa’adin Mako Biyu Kan Batun ƙarancin Albashi
Ƙungiyar kwadago ta bai wa gwamnonin jihohi wa’adin mako biyu su fara tattaunawa kan batun biyan ƙarancin albashin N35,000 ga ma’aikata a jihohinsu.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan wa’adin ya yi daidai da sharuddan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya, da ƙungiyoyin kwadago ta Najeriya suka sanya wa hannu.
Sassan Jihohin ƙungiyoyin ƙwadagon sun ba da wa’adin makonni biyu inda suka tuntubi gwamnonin da su hanzarta aiwatar da shirin biyan ƙarancin albashin.
Read Also:
A wani labarin kuma, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da shirin bada tallafin kudi naira tiriliyan 1 da nufin taimakawa gidaje miliyan 15 domin rage raɗaɗin tattalin arzikin da ake samu na cire tallafin man fetur.
A ƙarkashin wannan shirin, kowane magidanci zai karbi Naira 25,000 na tsawon watanni uku, wanda ya kai kusan naira tiriliyan 1.13.
Ministar ma’aikatar jin ƙai, Dr. Betta Edu, ta bayyana cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 61 ne za su ci gajiyar wannan tallafin kudi.
A baya dai shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun cimma matsaya da gwamnatin tarayya a ranar 1 ga watan Oktoba, inda ta tanadi cewa duk ma’aikatan tarayya za su karbi ƙarancin albashin naira 35,000 daga watan Satumba, har sai an kammala sabon mafi karancin albashi na kasa.