ƙarancin Mai da Takardun Kuɗi: NLC ta yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki
Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta bai wa gwamnatin ƙsar wa’adin mako ɗaya ta warware matsalar ƙarancin mai da takardun kuɗi da ake fama da su ko kuma ta tsunduma yajin aiki.
Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Joe Ajaero ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai game da taron da kwamitin gudanarwar ƙungiyar ya gudanar.
Read Also:
Ya ce ƙungiyar za ta shiga yajin aikin gama-gari idan aka gaza shawo kan matsalolin biyu cikin mako ɗaya.
Ajaero ya kuma yi tur da ƙarancin man fetur a ƙsar inda ya koka cewa matsalar ta kai ma’aikata da ƴan Najeriya bango.
A baya-bayan nan ne Kotun ƙolin ƙasar ta yi umarnin ci gaba da amfani da tsaffin takardun kudi na Naira 200 da 500 da 1,000 har zuwa ranar 31 ga watan Disamban shekarar da muke ciki ta 2023.
Sai dai har yanzu mutane na fuskantar ƙalubale wajen samun takardun kuɗi a hannunsu.