‘Yan Takarar Gwamna 6 na Jam’iyyun Adawa Sun Janyewa Fintiri

 

Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ƙara samun goyon baya bayan wasu yan takara na jam’iyyu 6 sun kai masa ziyara.

Yan takarar gwamna har su 6 sun amince zasu mara baya ga kudirin Fintiri na neman tazarce a zaben gwamna mai zuwa.

Fintiri na jam’iyyar PDP na fuskantar barazana mai girma daga Sanata Aishatu Binani, yar takarar gwamna a inuwar APC.

Adamawa – Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya samu gagarumin ƙarin goyon baya a kudirinsa na neman tazarce a zaben gwamna mai zuwa ranar Asabar.

Gwamnan ya samu ƙarin karfi ne bayan wasu ‘yan takarar gwamna 6 na jam’iyyun adawa a Adamawa sun amince za su mara masa baya domin tabbatar da ya samu nasara.

PM news ta tattaro cewa ‘yan takarar gwamnan guda 6 sun ayyana cikakken goyon bayansu ga gwamna Fintiri a Yola, babban birnin jihar Adamawa ranar Litinin.

Bugu da ƙari, sun umarci baki ɗaya magoya bayansu da mambobin jam’iyyun su, su zabi Ahmadu Fintiri, wanda ke neman tazarce a inuwar jam’iyyar PDP.

Jerin sunayen yan takarar da suka janye

Yan takarar da suka yanke shawarin janyewa bayan sun zauna da Fintiri sun haɗa da, Malam Bello Babajo na jam’iyyar APM, Malam Yahaya Chulde na APGA, da Emmanuel John-Yerima na NRM. Sauran su ne, Ambrose Zenith na Zenith Labour Party (ZLP) da kuma Babangida Furo na Action Democratic Party (ADC).

A madadinsu baki ɗaya, Mista Babajo, ya ce sun cimma matsayar mara wa gwamna mai ci baya ne bayan neman shawari daga masu ruwa da tsaki da magoya bayan jam’iyyunsu.

Ya ce gwamnatin Fintiri ta baiwa mara ɗa kunya musamman a bangaren ayyukan raya ƙasa, walwalar ma’aikata da kuma tsaro.

“Mun tsaida shawarin mara wa gwamnati mai ci baya saboda nasarorin da ta samu kuma zamu yi aiki don tabbatar da Fintiri ya zarce kan kujerar gwamna,” inji shi.

Ƙarin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here