Ribar da NNPC ta Samu a Karshen Shekarar 2020

 

NNPC ta bayyana ribar naira biliyan 287 da ta samu a karshen shekarar 2020, a karo na farko cikin shekaru 44 a tarihin kamfanin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ministan fetur ya sanar da hakan ne a wata takarda ta ranar Alhamis.

Buhari ya bayyana yadda asarar kamfanin ta rage daga naira biliyan 803 zuwa naira biliyan 1.7 daga shekarar 2019 zuwa 2020.

FCT, Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa tarihin da ba a taba kafa wa ba a tsawon shekaru 44 a tarihin kamfanin man futur din.

Shugaba Buhari ya bayyana yadda NNPC ta samu ribar naira biliyan 287 a karshen bisa kididdigar 2019 zuwa shekarar 2020, The Cable ta rawaito.

Shugaban kasan wanda shine kuma ministan man fetur ya bayyana wadannan tarin nasarorin a wata takarda ta ranar Alhamis, 26 ga watan Augustan 2021.

Buhari ya sanar da yadda asarar NNPC ta ragu daga naira biliyan 803 daga shekarar 2018 zuwa naira biliyan 1.7 a shekarar 2019 sannan daga karshe ya bayyana ribar da aka samu gaba daya a 2020.

A cewar Femi Adesina, kakakin shugaban kasa, a wata takarda ta ranar Alhamis kamar yadda ya yanko jawabin shugaban kasa:

“Ina farin cikin sanar da kacokan ribar da aka samu bayan cire haraji na shekarar 2020 da NNPC ta samu ta naira biliyan 287. An samu wannan bayanin ne bayan kididdigar duk shekara da aka kammala,”

An samu wannan nasarar ne sakamakon dagiya da zage damtsen shugaban kasa don mutanen Najeriya su amfana da romon da aka samu ta ma’adanan kasa.

“Na bai wa NNPC umarnin dinga sanar da duk wasu bayanai na kididdigar kudade kamar yadda doka ta tanadar don ko wanne dan Najeriya ya san halin da ake ciki.

“Ina taya ma’aikata da shugabannin kamfanin murnar samun wadannan nasarorin sannan muna fatan ci gaba da ganin irin haka a shekaru masu zuwa.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here