Goodluck Jonathan ya Zama Shugaban Jami’ar Cavendish ta Kasar Uganda

 

Tsohom shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya zama shugaban jami’ar Cavendish ta kasar Uganda.

Tsohon shugaban ya zama mutum na uku da zai jagoranci jami’ar tun bayan da aka kafa ta.

Rahotanni sun bayyana cewa Jonathan ya fara aiki nan take, inda ya jagoranci bikin yaye dalibai karo na 10.

Abuja – An rantsar da tsohon shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Jonathan, a matsayin sabon shugaban jami’ar Cavendish, Uganda.

Tsohon shugaban ya sanar da wannan cigaba da ya samu a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook, inda ya haɗa da wasu zafafan hotuna yayin rantsar da shi a sabon mukamin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Jonathan shine shugaban jami’ar Cavendish na uku tun bayan kafa makarantar.

A rubutun da Jonathan ya yi a facebook, yace:

“Ina farin cikim sanar da ku cewa an rantsar da ni a hukumance a matsayin shugaban jami’ar Cavendish, kuma har na fara gudanar da aiki na a wurin bikin yaye ɗalibai karo na 10 yau a Kamfala, Uganda.”

“Ina taya ɗaliban da aka yaye murna tare da rokon su da su yi amfani da ilimin su wajen tallafawa mutane, gina al’umma ta gari da kuma samar da cigaba a yankunansu.”

Shugabannin jami’ar da suka gabaci Jonathan

Tsohon shugaban ƙasar Zambia, marigayi Kenneth Kaunda, shine ya fara jagorantar jami’ar a karon farko bayan kafa ta.

Yayin da tsohon shugaban haɗaɗɗiyar jamhuriyar Tanzania, marigayi Benjamin Mkapa, ya zama shugaba na biyu da ya jagoranci jami’ar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here