Hira da Soja: DSS ta Sammaci ‘Yan Jaridar ChannelsTV

 

Gwamnati tarayya ta sammaci yan jarida zuwa Abuja.

Wannan ya biyo bayan wasikar tuhumar da hukumar NBC ta aikewa Channels.

Gwamnati na tuhumar ChannelsTV da yunkurin tayar da tarzoma a kasa.

Rahotanni na nuna cewa hukumar DSS ta sammaci wasu yan jaridar gidan talabijin ChannelsTV dake Legas kan hirar da sukayi da wani tsohon Soja mai suna, Kunle Olawunmi.

A cewar Arise News, daya daga cikin lauyoyin Channels TV na tare da yan jaridan dake hanyarsu ta zuwa Abuja yanzu haka.

Wani hira yan jaridan sukayi?

A ranar Talata, tsohon Sojan Ruwa, Commodore Kunle Olawunmi, a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta san wadanda ke daukan nauyin ‘yan ta’addan Boko Haram da suka addabi kasar.

Ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida a shirin Sunrise Daily na ChannelsTV.

Olawunmi yace:

“Su (gwamnati) sun sani. A Afrilun shekarar nan, gwamnati ta ce ta damke yan kasuwar canji 400 dake daukan nauyin yan Boko Haram. Haka suka fada mana.”

Hira da Soja: DSS ta Sammaci ‘Yan Jaridar ChannelsTV

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here