Jam’iyyar PDP ta Nada Sabon Shugaban Jam’iyyar na kasa

 

FCT, Abuja – Bayan kwanaki biyu ana dambarwa kan shugabancin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, an nada mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa (kudu), Yemi Akinwonmi a matsayin mukadashin shugaba.

Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ne ya sanar da hakan bayan taron sirri da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta yi a ranar Alhamis a Abuja, rahoton Premium Tiames.

Mr Akinwonmi zai maye gurbin shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, wanda ranar Litinin wata babban kotun jihar Rivers ta hana shi cigaba da zama shugaban PDP na kasa.

Ya tabbatar da sauya taron kwamitin masu gudanarwa na jam’iyyar wato NEC zuwa ranar Asabar.

Mr Ologbondiyan ya shaidawa manema labarai cewa:

“Kowa ya amince da nadin Elder Yemi Akinwonmi a matsayin mukadashin shugaban jam’iyya.

“Za mu yi taron mu NWC a gobe domin shirya babban taron mu na NEC misalin karfe 12 na ranar Asabar.”

Ku saurari karin bayani…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here