GEEP 2.0: Gwamnatin Tarayya Tayi Sabon Shirin Tsarin TraderMoni, MarketMoni da FarmerMoni

 

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta shigo da sabon samfurin tsari na GEEP 2.0.

Marasa karfi za su amfana da TraderMoni, MarketMoni, da kuma FarmerMoni.

An kuma kara kudin da ake rabawa matasa, manoma da kananan ‘yan kasuwa.

Abuja – Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin nan na Government Enterprise and Empowerment Programme wanda aka fi sani da GEEP.

The Cable tace wannan karo an yi wa shirin sabon tsari, aka sa masa suna GEEP 2.0 da nufin a ceto mutane miliyan 100 daga kangin talauci a Najeriya.

Ministar bada agajin gaggawa da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouq ta kaddamar da wannan shiri ranar Talata, 25 ga watan Agusta, 2021 a garin Abuja.

Sadiya Umar Farouq take cewa wannan shiri ya na cikin tsare-tsaren NSIP da gwamnatin tarayya ta shigo da shi domin tallafa wa marasa karfi da galihu.

Ministar tace wannan karo shirin GEEP zai tallafi wadanda ba su ci moriyar sauran tsare-tsaren da aka kawo domin taimaka wa ‘yan kasuwa da jari ba.

Abin da Ministar ta fada

“GEEP ya zo ne a samfurori uku – TraderMoni da aka kawo domin matasan da ba ayi da su, MarketMoni – na mata marasa karfi, sai FarmerMoni – wanda zai maida hankali a kan manoman da ke karkara.”

‘Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a yalwata tsarin, a bada bashin kudi ga karin mutane miliyan daya da za su ci moriyar shirin.”

“Za a maida hankali a kan kananan manoma a shekarar 2020/2021, an canza wa GEEP fasali, an kaddamar da tsarin GEEP samufuri na 2.0 a yau.”

“GEEP 2.0 zai taimaka wa mata, matasa marasa aikin yi, da sauran marasa galihu a cikin al’umma.”

“Ina so in bayyana cewa an tsara GEEP 2.0 da kyau wannan karo ta yadda aka samu wakilai daga tarayya, jahohi da kuma kananan hukumomin Najeriya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here