A Cikin Watanni 3 Tattalin Arzikin Najeriya ya Karu da 5.01%

 

Labari mai dadi dake bayyana shine na habakar tattalin arzikin Najeriya da kashi 5.01 a cikin watanni uku.

Kamar yadda rahoton NBS ya nuna, an samu wannan nasarar ne bayan dawowar harkokin kasuwanci bayan corona.

Kasar Najeriya ta fada kwata ne tun bayan da kasar ta wulla cikin matsalar karayar arziki a cikin shekarar 2016.

Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 5.01 a tsakanin watan Afirilu zuwa watan Yuni na 2021 daga kashi 0.51 da aka samu a watanni uku na farkon shekarar nan.

Rahoton daukacin kayan aiki da kasar nan ta samar a na watanni uku wanda aka NBS ta fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa wannan cigaban na kashi 5.01% shine mafi girma da aka taba samu tun daga karshen shekarar 2014, Daily Trust ta rawaito.

Wannan habakar tattalin arzikin ya fi na wancan shekarar 2020 da ta gabata tare da ta watanni uku na farko na wannan shekarar da aka gani.

Daily Trust ta rawaito cewa, rahoton karuwar tattalin arzikin labari ne mai dadi kuma alamun nasarar ne da ya bayyana shekarar 2021.

Rahoton ya ce wannan alamu ne na dawowar kasuwanci da al’amuran tattalin arziki bayan aukuwar muguwar annobar corona.

NBS ta kara da bayanin cewa:

Farfadowar tattalin arzikin kasar nan da ya fara daga karshen 2020, tare da dawowar al’amuran kasuwanci a gida Najeriya da duniya baki daya, shine silar cigaban da ake gani.

Kiyasi kan rahoton ya nuna cewa bangaren da ba na man fetur ba ya samar da kashi 6.74 inda sauran kashin an samo shi ne daga kasuwanci, yada labarai da sadarwa, sufuri da sauransu kamar yadda rahoton ya sanar.

Tattalin arzikin Najeriya ya fada wani hali tun a shekarar 2016 yayin da kasar ta fada matsalar karayar tattalin arziki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here