Tin 2015: Gwamna Ganduje da Rabi’u Kwankwaso Sun Hadu

 

Abokan siyasa da suka zama abokan hamayya sun sake haduwa da juna.

Kwankwaso ya kasance maigidan Ganduje na tsawon shekaru amma abubuwa suka tabarbare tsakaninsu.

Jiga-jigan siyasan biyu zasu hau jirgi daya zuwa Kano.

Abuja – Gwamnan jahar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da magabacinsa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso sun hadu bayan shekara da shekaru.

Tsofaffin abokan siyasan sun hadu ne a sashen VIP na tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja, DailyNigerian ta rawaito.

Sun zauna dakin ne yayinda suke shirin hawa jirgi don zuwa jahar Kano.

Jagororin biyu sun dade suna wasan buya tun lokacin da suka samu sabani bayan zaben 2015.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here