Sabuwar Dokar da Kungiyar Taliban ta Fiyar a Kasar Afghanistan

 

Kungiyar Taliban a Afghanistan ta bayyana sabuwar doka ga mata da kuma mutanen kasar.

Kungiyar ta ce ta haramta kida, sannan mata ba za su yi tafiya mai nisa sai da rakiyar namiji.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa, mata na da damar zuwa aiki, asibiti da kuma makaranta.

Afghanistan – Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar da haramta kida a Afghanistan saboda “Ba Musulunci ba ne”.

Wannan batu na kunshe ne a cikin wata hira da jaridar New York Times da kakakin kungiyar Taliban, Zabiullah Mujahid, a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta, Ripples Nigeria ta rawaito.

Sai dai ya lura cewa Taliban na fatan shawo kan mutane su yi biyayya ga sabuwar dokar, maimakon tilasta musu.

Haramcin zai zama kamar dawo da daya daga cikin tsauraran dokoki na mulkin kungiyar Taliban ta 1990, lokacin da aka hana yawancin nau’ikan kade-kade, ban da wakokin addini.

Babban mai magana da yawun kungiyar ya sanar da sabon haramcin a wata hira inda yayi kokarin jaddada cewa Taliban ta canza daga tsaurin gwamnatinta na farko.

Zabiullah Mujahid ya fadi cewa:

“An haramta kida a Musulunce, amma muna fatan za mu iya shawo kan mutane cewa kar su aikata irin wadannan abubuwa, maimakon tilasta musu.”

‘Yan Taliban sun halasta wakokin addini a lokacin tsohuwar gwamnatinsu ta farko, amma suna daukar wasu nau’ikan kade-kade a matsayin abin jan hankali wanda zai iya karfafa tunani mara kyau.

Mata ba za su yi tafiya mai nisa sai da rakiyar namiji

Mata a Afghanistan za su bukaci namiji a matsayin dan rakiya don yin balaguron da ya wuce fiye da kwana guda, in ji wani shugaban Taliban.

Mujahid ya ce gwamnatin za ta kasance mai sassaucin ra’ayi sabanin yadda ta kasance a baya wajen sanya dokoki kan mata kamar yadda ta ke neman karbuwa daga kasashen duniya a yanzu, jaridar Mirror ta rawaito.

Acewarsa, amma a lokaci guda ya kamata mata su zauna a gida na dan lokaci; ra’ayin da masu sukar Taliban suka ce shine abin da ya faru lokacin da suka yi mulkin farko.

Mujahid ya kuma yi ikirarin cewa mata za su iya ci gaba da aiki muddin sun rufe fuskokinsu.

A karkashin mulkinsu na baya ‘yan Taliban sun tilastawa mata sanya cikakkiyar burqa wacce ke rufe kai da fuska da raga da ke rufe idanu.

Kakakin na Taliban ya kuma ce za a bai wa mata damar zuwa makaranta, aiki da asibitoci amma za su bukaci a yi musu rakiya tare da wani namiji ga duk wasu tafiye-tafiye masu nisa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here