NNPCL Zai Daina Shiga Tsakanin Ƴan Kasuwa da Matatar Dangote

 

FCT, Abuja – Kamfanin man fetur na NNPCL ya fitar da sabuwar sanarwa kan alakarsa da matatar Dangote.

NNPCL ya ce zai daina shiga tsakanin yan kasuwa da matatar Dangote a kan abin da ya shafi cinikin mai.

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa NNPCL ya ce duk wata matata a Najeriya za ta iya kulla ciniki da yan kasuwa.

Matatar Dangote: Majalisa ta yi kira ga NNPCL

Tun a ranar 26 ga Satumba majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan NNPCL da matatar Dangote.

Majalisar ta bukaci gwamnati ta tilasta kamfanin NNPCL ya cire hannu kan shiga tsakanin yan kasuwa da matatar Dangote.

Dan majalisa daga jihar Bayelsa, Hon. Oboku Oforji ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisar wakilai inda ya ce ba adalci a cikin lamarin.

NNPCL ya dauki mataki kan matatar Dangote

Kamfanin NNPCL na gwamnatin tarayya ya ce zai ajiye matsayin mai shiga tsakani a harkar cinikin mai a matatar Dangote.

NNPCL ya ce daga yanzu yan kasuwa za su iya kulla ciniki tsakaninsu da matatar Dangote ba tare da katsalandan ba.

Yiwuwar saukar farashin man fetur

Masana na ganin hakan zai iya kawo saukar farashin man fetur a gidajen man Najeriya kasancewar za a samu gasa a tsakanin yan kasuwa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa biyo bayan hukuncin, fetur ya sauko daga N1,300/1,350 zuwa N1,200/1,150 a jihar Abia.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here