Kungiyar NPYA ta Shawarci Gwamnonin Arewa da su Hada Kudi Domin Kafa Banki na Yankin a Maimakon Dogaro da na Kudu

 

Wata kungiyar matasa masu muradin kare al’ummar Arewa-maso-gabas ta yi gargadin cewa tattalin arzikin yankin na daf da durkushewa.

Kungiyar ta bada shawarar cewa ya kamata gwamnonin arewa su hada kudi domin kafa wata banki na yankin a maimakon dogaro da na kudu.

A cewar kungiyar, kiraye-kirayen da gwamnonin kudu ke yi na ba basu damar su rika karbar harajinsu ya isa zama darasi ga gwamnonin yankin.

Wata kungiyar matasan arewa idan har jahohin Arewa-maso-gabas, NPYA, ta ce ya zama dole jahohin yankin su rubanya harajin da suke samu, su kuma kafa banki domin tallafawa yankin idan ana son kawo karshen talauci, rashin aiki da matsalar tsaro, The Sun ta rawaito.

Kungiyar cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Sabiu Tirzimi, ta bada shawarar jahohin Arewa-maso-gabas su bude wani asusu don zuba Naira biliyan biyar-biyar, da za a iya assasa babban bankin kasuwanci na bai-daya.

NPYA ta yi kira a yi koyi darasi daga Gwamnan Bauchi

A kan bukatar gwamnonin na kudu maso gabas su habaka hanyoyin kudin shiga, kungiyar ta yi kira ga gwamnonin su yi koyi da irin tsare-tsaren da Gwamna Bala Muhammad na jahar Bauchi yake aiwatarwa wajen tattara haraji da ke bashi daman yi wa jama’arsa aiki.

Hakazalika, sanarwar ta bayyana cewa gwamnatocin tarayya da suka gabata sun gaza cika wa yankin alkawurra da suka dauka, musamman na aikin Wutar Mambila wanda ya yanzu ya zama labarin kanzon kurege.

Sanarwar ta bayyana cewa muddin gwamnonin ba su yi hakan ba, to sauran bankunan kasuwanci guda 30, na ‘yan kudancin kasar nan za su ci gaba da mamaye ko’ina a yankin, Leadership ta rawaito.

A cewar kungiyar:

“Kiraye-kirayen da gwamnonin yankin kudu ke yi a kafafen watsa labarai kan neman a basu damar karbar harajinsu ya kamata ya zama darasi ga gwamnonin arewa su habaka hanyoyin samun kudin shiga ko kuma su fada matsala na dogaro da gwamnatin tarayya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here