Obasanjo ya Caccaki Hukuncin da Alƙalan Najeriya Suka Yanke Kan Shari’o’in Zaɓe
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya caccaki hukuncin da alƙalan Najeriya suka yanke kan shari’o’in zaɓe, yana mai cewa bai kamata alƙalai uku zuwa biyar su soke hukuncin da miliyoyin masu kada ƙuri’a suka yanke a lokacin zabe ba.
Obasanjo ya bayyana ikon da wasu alƙalai ƙalilan ke da shi a matsayin al’amari da “ba za a amince da shi ba.”
Read Also:
Tsohon shugaban ƙasar ya yi magana ne dangane da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ke ci gaba da yi kan taƙaddamar zaɓe ta bayan zaɓen 2023 a Najeriya.
A makon da ya gabata ne dai wasu alƙalan kotun ɗaukaka ƙara suka yanke hukuncin korar wasu gwamnoni uku daga aiki.
Lokacin da yake tsokaci a wani taro sake fasalin dimokuraɗiyya domin amfanin ƙasashen Afirka, a garin Abeokuta na jihar Ogun, ya ce tsarin mulkin dimokuraɗiyya na ƙasashen yamma ba zai taɓa yin daidai da ƙasashen Afirka ba kasancewar ba ya la’akari da ra’ayin mafi yawan al’umma.