APC na Amfani da ƙarfin Iko: Fadar Shugaban Najeriya ta Mayar wa da Atiku Martani

 

Fadar shugaban Najeriya ta mayar wa babbar jam’iyyar adawa ta PDP da kuma ɗan takararta na shugaban ƙasa Atiku Abubakar kan zargin da suka yi cewa jam’iyyar APC mai mulki na “amfani da ƙarfin iko” wajen tanƙwara hukuncin kotuna.

Wata sanarwa da mai taimakawa shugaba Tinubu kan fannin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya ce abin da PDPn da ɗan takararta ke yi shure-shure ne da ba zai hana mutuwa ba, inda ta ce tun bayan shan kaye a zaɓe da jam’iyyar tayi, su ke ta ƙoƙarin cin mutuncin ɓangaren shari’a da kuma yin zarge-zargen da ba su tushe balle makama kan shugaban Najeriya.

Sanarwar ta ce Atiku da jam’iyyarsa sun ƙasa yin bincike yadda ya kamata kafin fitowa fili da yin zarge-zarge marasa kan gado.

“Sun yi zargin cewa lokacin da Tinubu yake gwamnan Legas, ya take hakkin ƴan adawa, ya riƙa bai wa ɓangaren shari’a cin hanci da kuma son mayar da ƙasar kan tsarin jam’iyya ɗaya ta hanyar naɗa masu yi masa mubaya’a a matsayin kwamishinonin hukumar zaɓe. Duk waɗannan zarge-zarge ba su da gaskiya,” in ji sanarwar.

Fadar shugaban Najeriyar ta ce shugaba Tinubu hakikanin ɗan dimokuraɗiyya ne, kuma bai taɓa yi wa ɓangaren shari’a katsalanda ba a hukunci da take yanke wa.

“A nan a idon kowa mun ga yadda ɗan takarar gwamna na PDP a jihar Osun ya kayar da jam’iyyar APC a kotun koli. Duka wannan ya faru ne lokacin Tinubu,” in ji fadar shugaban Najeriyar.

Har ila yau, sanarwar ta ce Tinubu ba shi da niyyar mayar da ƙasar kan tsarin jam’iyya ɗaya kamar yadda Atiku da jam’iyyarsa ke zargi ba.

Fadar shugaban ƙasar ta ce ana waɗannan zarge-zarge ne kawai don kawo ruɗani a ƙasar.

‘Shari’ar kotunan Najeriya ta zama tufka da warwara’

A ranar Litinin ne babbar jam’iiyyar adawa ta PDP da ɗan takararta na shugaban ƙasa Atiku Abubakar suka bayyana hukunce-hukuncen da kotunan ɗaukaka ƙara suka yi, inda suka ƙwace nasarar wasu gwamnoni a matsayin “karan-tsaye” ga dimokraɗiyya.

Jam’iyyar adawar na zargin APC mai mulkin Najeriya ne da “amfani da ƙarfin iko” wajen tanƙwara hukuncin kotunan, zargin da APC ta musanta.

“Shari’ar Najeriya ta zama kamar rawar ‘yan mata yanzu; idan an yi gaba, sai a koma baya,” in ji Mataimakin Sakataren PDP na Ƙasa, Ibrahim Abdullahi.

Ya ce dalilan da mutanen nan ke gabatarwa suna kwace zaben nan, akasari batutuwan da suka shafi kafin zabe ne. A cewarsa, kotun koli ta yanke hukunci da cewa: “Ba abubuwa ba ne da suka shafe ta, a hukuncin da ta bayar kan dan takararmu, Atiku Abubakar”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com