Jaroslav Silhavy ya yi Ritaya Daga Kocin Czech

 

Jaroslav Silhavy ya yi ritaya daga aikin kocin Jamhuriyar Czech, bayan kasar ta samu gurbin shiga Euro 2024.

Silhavy, mai shekara 62 ya kai kasar matakin daf da na kusa da na karshe a Euro 2020, wanda ya karbi aikin tun cikin Satumban 2018.

Jamhuriyar Czech ta samu gurbin shiga wasannin da Jamus za ta karbi bakunci a shekara mai zuwa, bayan da ta ci Moldova 3-0 ranar Litinin.

”Ko da yake muna cike da murna, tun a baya mun cimma matsaya tun kafin wasannin cewar kowa zai kama gabansa.” kamar yadda ya sanar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com