Shin da Gaske Obasanjo na Goyan Bayan Peter Obi a Zaben 2023

 

Wata majiya da aka yi imanin tana da kusanci da tsohon shugaban kasa Obasanjo ta ce jagoran kasar na kokarin tabbatar da darajarsa ne a matsayin uban kasa a tarihin Najeriya.

An rahoto cewa Obasanjo yana da ra’ayin cewa lokaci ne da ya kamata yankin kudu maso gabas ta fitar da shugaban kasa.

An ce tsohon shugaban kasar yana goyon bayan Peter Obi ya zama shugaban kasa na gaba, don haka ya ke tuntubar masu ruwa da tsaki gabanin zaben.

Gaskiya ta fito game da ganawar da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi da wasu yan takarar shugaban kasa.

Wani majiya da ya hallarci taron Nyesome Wike na Rivers, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia da Samuel Ortom na Benue ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar na son tabbatar da matsayinsa na uban kasa a tarihin Najeriya, This Day ta rahoto.

Obasanjo ya gana da bangaren Wike na jam’iyyar PDP a Landan

Tsohon shugaban kasar ya gana da gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike da bangarensa na jam’iyyar PDP, inda suka tattauna kan babban zaben 2023.

Obasanjo, duk da cewa ya musanta yana goyon bayan wani dan takara, akwai alamu da ke nuna yana goyon bayan Peter Obi, dan takarar jam’iyyar LP.

Majiyoyi sun ce dalilinsa shine yin dai-daito da ‘adalci’ na mulki ga manyan kabilun kasar duba da cewa Igbo ba su yi shugaban kasa ba bayan dawowar demokradiyya tun 1999.

Tsohon shugaban kasar a baya-bayan nan ya yi alkawarin zai sanar da yan Najeriya ajandarsa game da babban zaben.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci tsaffin shugabannin kasa, Abdulsalami Abubakar da Ibrahim Babangida.

Daya daga cikin wadanda suka hallarci taron kuma aka imanin yana da kusanci da Obasanjo ya ce:

“Obasanjo na goyon bayan Obi ne saboda ya jadada matsayinsa a tarihin Najeriya, a matsayin dan kasa mara kabilanci.Yana ganin ya kamata a bawa Igbo dama tunda Hausawa da Yarbawa sun yi mulki. Don haka, ya ke goyon bayan Obi.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here