Takardun Makaranta na Bogi: ICPC ta Kara Gayyatar Okai Obono-Obla
Hukumar bincike akan rashawa da sauran laifuka mai zaman kanta ta ICPC, ta kara karar tsohon hadimin Buhari, Okoi Obono-Obla.
Hakan ya faru ne a ranar Litinin bisa zargin sa da amfani da takardun makaranta na bogi, a babbar kotun jahar Filato.
Ana zargin sa da amfani da sakamakon jarbawar bogi wurin neman gurbin karatu akan shari’a a jami’ar jahar Jos (UNIJOS).
Filato – Hukumar bincike akan rashawa da sauran laifuka mai zaman kan ta, ICPC, ta gayyaci tsohon hadimin shugaban kasa, Okoi Obono-Obla, bisa laifin amfani da takardun makaranta na bogi.
Hukumar ta maka karar Obono-Obla a ranar Litinin, a babbar kotun jahar Filato da ke Jos kamar yadda NewsWireNGR ta rawaito.
An zarge shi da amfani da takardun makaranta na bogi don neman gurbin karatu a fannin shari’a a jami’ar jahar Jos (UNIJOS).
Takardar bogi da ya yi amfani da ita tana daya daga cikin laifuka 10 da ake zargin sa dasu ciki har da zargin sa da rashawa, dama tun ranar 1 ga watan Yulin 2020 ICPC ta maka shi babbar kotun Abuja. Saidai daga baya hukumar ta janye karar bisa ruwayar NewsWireNGR.
Har ila yau hukumar ta kara maka shi a kotu
A ranar 8 ga watan Yulin 2020 hukumar ta kara maka shi a babbar kotun FCT, tare da Mr Obono-Obla, tsohon hadimin shugaban kasa na musamman har da Aliyu Ibrahim da darektan ABR Global Petroleum Resources Ltd, Daniel Omughele Efe.
Sannan a ranar 4 ga watan Maris din 2021, hukumar ta kara sabunta karar, yayin da ta cire korafin amfani da takardar bogi da sauran korafi 3 na zargin sa da rashawa.