Kungiyar CAN ta Zabi Rev.Daniel Okoh a Matsayin Sabon Shugabanta

 

An zabi Babban Rev. Daniel Okoh a matsayin sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN.

Wa’adin shugaban Kungiyar CAN mai Martaba Samson Olusupo-Ayokunle da sauran shugabannin zartarwa na kasa dake cikin tawagarsa ya zo karshe.

Shugaban CAN mai barin gado ya godewa daukacin ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da addu’o’in da suke mi shi.

Abuja – An zabi Babban Rev. Daniel Okoh a matsayin sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN.

Rahoton The Guardian Sanarwar hakan na kunshe ne a wata jawabi da babban sakataren kungiyar ta CAN, Mista Joseph Daramola ya fitar jiya a Abuja.

Okoh shine Babban Shugaban Cocin Christ Holy Church, wanda kuma ake kira Nation Builders (Odozi-Obodo).

CAN ta ƙunshi ƙungiyoyi biyar wanda ya hada da Majalisar Kirista ta Najeriya (CCN), Sakatariyar Katolika ta Najeriya (CSN), Fellowship Christian Pentecostal of Nigeria (CPFN)/Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN), Ƙungiyar Ikklisiya ta Afirka (OAIC), TEKAN da ECWA Fellowship.

Kungiyar kiristocin Najeriya ta shirya gudanar da babban taronta a ranar 27 ga watan Yuli, wanda zai kafa sabuwar gwamnati. Majalisar ta kuma kawo karshen wa’adin Mai Martaba Samson Olusupo-Ayokunle da sauran shugabannin zartarwa na kasa a cikin tawagarsa.

Shugaban CAN mai barin gado ya godewa daukacin ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suka ba shi da kuma addu’o’in da suka mi shi, wanda ya sa ya samu nasarar gudanar da aikinsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here