Gwamna Ifeanyi Okowa ya yi Rashin Mai ba Shi Shawara na Musamman Kan Ci Gaban Kasuwanci

 

Gwamnatin jahar Delta baki daya ta fada cikin jimamin mutuwar Mary Iyasere.

Har zuwa mutuwarta, Iyasere ita ce mai ba da shawara na musamman ga Gwamna Ifeanyi Okowa kan bunƙasa harkokin kasuwanci.

Iyasere ta taba zama kwamishinar kasuwanci da yawon bude ido a lokacin mulkin gwamnan na farko.

Delta – Gwamna Ifeanyi Okowa na jahar Delta a ranar Laraba, 22 ga watan Satumba, ya rasa mai ba shi shawara na musamman kan ci gaban kasuwanci, Mary Iyasere.

Daga baya Marigayiya Iyasere wacce ta yi aiki a matsayin kwamishinar kasuwanci da yawon shakatawa na jahar a lokacin gwamnatin Gwamna Okowa na farko, ta koma kan mukamin da take kai har zuwa mutuwarta, The Nation ta rawaito.

A zahiri, mutuwar Iyasere ta kawo baƙin ciki ga ubangidanta, membobin majalisarsa, da gwamnatin jahar.

Marigayiyar lauyar wacce ta fito daga garin Urhuakpor, ta kasance cif ta Urhobo a masarautar Agbon.

Wataƙila za a fi tunawa da ita kasancewar ita ce ta kafa kungiyar Urhuakpor Women in Politics (UWIP) ta karamar hukumar Ethiope East.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here