Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bada Kwararun Shawarwari Guda Hudu

 

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayar da manyan shawarwari ga ‘yan Najeriya.

Ya ce wajibi ne ayi hobbasa wurin kawo karshen tabarbarewar tsaro a kasar nan baki daya.

Obasanjo ya ce ya kamata a dage wurin yin ayyuka tukuru don kawo karshen talauci a Najeriya.

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayar da sakonsa na sabuwar shekara ga ‘yan Najeriya.

Ya ce lokaci ya yi da shugabannin Najeriya za su mike tsaye wurin tabbbar da sun yi gyara akan yadda tattalin arzikin kasa ya tabarbare.Obasanjo yayi wannan maganar ne a Abeokuta, jihar Ogun.

1. Ya ce wajibi ne su tsaya tsayin-daka wurin ganin sun kawo karshen rashin tsaro a Najeriya, saboda al’amarin kullum kara lalacewa yake yi, babu birni babu kauye.

2. Ya yi kira ga gwamnati da su shiga harkar noma don tallafa wa kasa da samun cigaba a 2021. Wajibi ne a dage a gona don gudun kada ‘yan Najeriya su dinga kwana da yunwa.

3. Ya kara da cewa, Najeriya tana bukatar addu’a, ta haka ne za a kawo karshen tashin hankalin da kasar nan take ciki. Sai dai ba addu’a kadai za a tsaya ba, wajibi ne a mike tsaye kuma a yi aiki tukuru. Tabbas za a samu nasarar idan aka yi hakan a 2021.

4. Ya kuma bayyana damuwarsa a kan rashin tsaro da kuma annobar COVID-19 mai kawo cikas ga tattalin arzikin kasa. Ya ce hakan ne babban kalubale, wanda ya janyo tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here