Gwamna Ortom ya Caccaki ‘Yan Jam’iyyar APC a Jaharsa

 

Gwamnan jahar Benue, Samuel Ortom ya caccaki ‘yan jam’iyyar APC a jaharsa, inda ya kira su da mashaya barasa.

Gwamnan ya bayyana haka ne jiya Asabar, lamarin ya kuma kawo cece-kuce daga ‘yan jahar tasa ta Benue.

Gwamnan ya bayyana dalla-dalla cewa, ‘yan APC ne ke kitsa komai na batanci da jawo masa zagi a jahar.

Benue – Biyo bayan cece-kucen da ya biyo bayan kalaman da ya yi kan wasu ‘yan jaharsa da ya bayyana a matsayin ‘yan barasa, Gwamna Samuel Ortom na jahar Benue ya yi karin haske.

A lokacin da yake kaddamar da sabon ginin Cocin Embassy na RCN a Makurdi, babban birnin jahar Benue, gwamnan ya ce wasu ‘yan jaharsa da ke wuni suna shan barasa suna ci gaba da cin mutuncinsa, Daily Trust ta rawaito.

Da dama dai sun bayyana hakan a matsayin abin da bai kamata ba, inda suka soki gwamnan da kuma zarginsa da rashin mutunta ‘yan jahar.

Sai dai a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Nathaniel Ikyur ya fitar a madadin sa, gwamnan ya ce batun naaa tsokaci ne ga ‘ya’yan jam’iyyar APC a Benue.

Ikyur ya ce kalaman Ortom kan wasu mutane ne da suka kulla sharri a cikin zukatansu akansa. “Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa labarin, musamman ma taken labarin ba gaskiya bane gaba daya da kuma kokarin bata sunan gwamnan.”

“Gwamnan ya bayyana karara cewa mafi yawan al’ummar Benue sun sani kuma sun yaba da gagarumin ci gaban da yake kawo musu.”

Kafin karin bayanin, Samuel Ortom ya ce tun farko bai so sake tsayawa takara a zaben 2019 saboda zagin da yake sha daga ‘yan adawar sa.

Ya kuma bayyana cewa, shi zababben ubangiji ne, don haka ‘yan jahar tasa ya kamata su daina zaginsa haka siddan, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Ya ce sai da yayi azumin wata uku, inda ya ce ubangiji ya ba shi umarnin sake tsayawa takarar gwamna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here