Ceto Matar Kwamishina da Direbanta: Gwamnan Jahar Benue ya Yabawa ‘Yan Sandan Jaharsa

Gwamna Ortom ya bada umurnin a rushe gidan da aka yi amfani da shi wurin ajiye matar kwamishina da aka direbanta da aka sace.

Gwamnan na jahar Benue ya bada umurnin ne bayan yan sanda sun ceto wadanda aka sacen a ranar Litinin 2 ga watan Agusta.

Ortom ya yi bayanin cewa an dauki matakin ne bisa tanadin dokar jahar Benue da ta shafi garkuwa da mutane

Makurdi, Jahar Benue – Gwamnan jahar Benue ya bada umurnin a rushe gidan da yan sanda suka kashe mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sannan suka ceto matar kwamishina da direbanta.

Legit.ng a baya ya ruwaito cewa jami’an tsaron Operation Zenda a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta sun kashe masu garkuwa da mutane biyu suka ceto Mrs Ann Unnege, matar kwamishinan kasa da sifiyo.

The Punch ta ruwaito cewa Gwamna Samuel Ortom wanda daga bisani a ziyarci hedkwatar yan sanda a Makurdi ya bada umurnin a rushe gidan da aka ajiye wadanda aka yi garkuwan da su.

Ya yi bayanin cewa hakan ya yi dai-dai da tanadin dokar hana satar mutane, garkuwa, kungiyoyin asiri da sauransu a Benue.

Legit.ng ta gano cewa ginin yana unguwar BIPC Quarters, ne a Nyinma Layout, Makurdi kuma an rushe ginin bayan umurnin gwamnan.

An bukaci masu gidajen haya su rika bincike kan mutanen da za su bawa gidajensu haya Da ya ke magana kan lamarin, mashawarcin Gwamna Ortom kan tsaro Kwanel Paul Hemba (mai murabus) ya bukaci masu gidaje su rika bincike kan mutane kafin su basu gidajensu haya.

Hemba ya ce za a kwace izinin gini a filin da aka gina gidan kamar yadda dokar jahar ta tanada.

Gwamna Ortom ya yabawa yan sanda, yana mai cewa jarumtar da suka yi zai zama darasi ga sauran bata gari cewa jahar Benue ba matattaran masu laifi bane.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here