Matsayin Aro: Osimhen ya Koma Galatasaray
Dan wasan gaban Napoli Victor Osimhen ya koma ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya a matsayin aro.
Dan wasan mai shekara 25 an ta yaɗa cewa zai koma ƙungiyar Chelsea da ke buga Premier Ingila.
Kazalika an riƙa alaƙanta shi da Al-Ahli ta Saudiyya har zuwa ranar Juma’a ranar ƙarshe ta rufe kasuwar musayar ‘yan wasa a Turai.
Sai dai har aka rufe kasuwar duka bai tafi ko wacce ƙungiya ba daga cikinsu.
Read Also:
Dan wasan Najeriyan ya ci kwallo 76 a wasa 133 da ya buga wa Napoli, kuma ya taka muhimmiyar rawa a Nasarar da ta samu ta lashe Serie A a 2022-23, inda ya ci kwallo 26.
Sai dai a bara ya gaza kai wa inda ake tsammani a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan wasa mafi ƙoƙari a Turai, inda ya ci kwallo 15 kacal.
Antonio Conte wanda shi ne kocin Napoli na yanzu, ya ɗauki dan wasan gaban Belgium da Chelsea, Romelu Lukaku mai shekara 31 kan kuɗin fan miliyan 30.
An samu rashin jituwa tsakanin Victor Osimhen da kungiyarsa ta Napoli, abin da ya kai ga cire sunansa daga cikin tawagar ‘yan wasan da za su buga musu kakar Serie A ta bana.