Tsaron Jihar Oyo na Cikin Matsala Idan Har Gwamna Makinde ya Zarce a 2023 – APC
Jam’iyyar APC a jihar Oyo ta yi gargaɗin cewa tsaron jihar na cikin matsala idan har gwamna Makinde ya zarce a Ofis a 2023.
A wata sanarwa, APC mai adawa a jihar ta ce daga zuwan Makinde ya lalata duk wani tubalin zaman lafiya da tsohon gwamna ya gina.
Wannan na zuwa ne a lokacin da wani bidiyo da watsu a kafafen sada zumunta wanda wani ya yi barazana ga rayuwar dan takarar APC.
Oyo – Jam’iyyar APC reshen jihar Oyo ta ce tsaron jihar zai lalace baki ɗaya matukar mutane suka sake dangwalawa Gwamna Seyi Makinde ya zarce zango na biyu a Ofis a zaɓen 2023.
Punch ta rahoto cewa APC ta yi wannan furucin ne a wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na jiha, Alhaji Tajudeen Olanite, ya fitar kuma aka raba wa manema labarai a Ibadan ranar Litinin.
Jam’iyyar hamayya a jihar watau APC ta soki gwamnan da amfani da kayan gwamnati wajen tallafa wa yan Daba, waɗan da ake zargin suna da hannu a kashe-ƙashen bayin Allah a Oyo.
Haka kuma Sajataren APC ya yi Allah wadai da barazanar kisan da aka yi wa ɗan takararsa na gwamna a 2023 kuma shugaban kwamitin ayyukan karkara a majalisar Datttawa, Sanata Teslim Kolawole Folarin.
Read Also:
A cewarsa ɗaya daga cikin jami’an gwamnatin Makinde, wanda aka naɗa a 2020, Alhaji Mukaila Lamidi, wanda ya fi shahara da sunan ‘Auxiliary’, shi ne ya yi barazana ga rayuwar Folarin a wani bidiyo da ya watsu kuma gwamna ya yi gum.
A sanarwan, APC ta ce barazana ga rayuwar ɗan takarata ba ɓoyayyen abu bane kasancewar bidiyon ya watsu a kafafen sada zumunta a yan kwanakin nan, Sunnews ta rahoto.
Wani sashin sanarwan ta ce:
“Gwamna Makinde bai cancanci ya zarce zango na biyu ba domin a mulkinsa na farko ya ɓata jihar nan ba dabanci da rikice-rikice, wanda gwamnan da ya gada, Marigayi Abiola Ajimobi, ya magance a lokacin mulkinsa na shekara 8.”
“Bayan barzana ga rayuwar mai girma Sanata Folarin, wannan Munkaila Auxiliary da wasu yan daba sun ragargaza allunan hoto da fastocin jam’iyyun hamayya, musamman babbar jam’iyyar adawa ta jihar.”
“Auxiliary ya jima yana jagorantar yan daba da makamai suna kakkarya allunan tallan APC da Fastoci a Ibadan da sauran sassan jihar.”
Muna kira hukumar yan sanda ta yi abinda ya dace – APC
A cikin sanarwan, Sakataren APC ya ce cikin ƴan watanni bayan zama gwamna, Makinde ya rusa tubalin zaman lafiya da tsohon gwamna na APC ya gina tsawon shekara 8.
“Saboda haka muna kira ga kwamishinan yan sanda na Oyo, Sufeta Janar na yan sandan ƙasar nan da su yi gaggauta yin abin da ya dace game da barzanar kisa ga Sanatan da ya shafe zango uku a majalisar Datttawa.”