‘Dan Kwallon Kafa, Mesut Ozil ya Sanar da Yin Ritaya Daga Buga Tamaula
Tsohon dan kwallon tawagar Jamus, Mesut Ozil ya sanar da yin ritaya daga taka leda.
Tsohon dan kwallon Real Madrid da Arsenal ya rataye takalmansa yana da shekara 34 da haihuwa.
Ozil ya fara taka leda a Schalke 04 daga nan ya koma Werder Bremen, sai dai ya taka rawar gani a gasar kofin duniya da aka yi a 2010.
A wasan ne ya fito da kansa, inda Jamus ta ci Ingila 4-1 a wasan quarter finals, hakan ya sa Real Madrid ta dauke shi.
Read Also:
A shekara ukun da ya yi a Sifaniya ya dauki La Liga karkashin Jose Mourinho, daga nan Arsenal ta saye shi a matakin mafi tsada a Emirates a 2013.
Ya taka rawar gani karkashin Arsene Wenger, amma sai Unai Emery bai samu dama ba, wanda ya rasa gurbinsa karkashin Mikel Arteta.
Ozil wadda ya buga wasa tare da Arteta a Arsenal ya koma Fernerbahce a 2021.
Bayan wasa 32 da ya yi sai ya koma Istanbul Basaksehir, wadda ya yi wa karawa hudu kacal.
Ozil ya lashe kofin duniya a tawagar Jamus a 2014, sannan ya yi ritaya a 2018, bayan wasa 92 da ya yi mata.