Jam’iyyar PDP ta Nemi Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele da ya Bar Ofis

 

Jam’iyyar PDP ta bayyana bukatar gwamnan CBN ya bar ofis saboda barnar da ya yiwa kasa.

PDP ta ce, APC da gwamnan su suka lalata darajar Naira a duniya, don haka kawai ya bar ofis.

PDP ta fadi haka ne a yau Alhamis a Sakateriyar Jam’iyar da ke babban birnin tarayya Abuja.

Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele yayi murabus cikin gaggawa, Daily Trust ta rawaito.

Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis 23 ga watan Satumba a Sakateriyar Jam’iyyar ta Kasa da ke Abuja.

Ya ce lokacin Emefiele a matsayin Gwamnan Babban Bankin CBN a karkashin gwamnatin APC ya gamu da gazawar manyan tsare-tsare na kudi, inda PDP ta bukaci ya bar ofishinsa na gwamnan CBN cikin gaggawa.

Ologbondiyan ya ce abin koyi ne a lura cewa lokacin da Emefiele ya hau kujerar Gwamnan Babban Bankin Najeriya a 2014 darajar Naira ta kasance N164 idan aka kwatanta da dalar Amurka.

A cewar Ologbondiyan:

“A yau, a hannun Emefiele da APC, Naira ta durkushe zuwa kusan N600 zuwa dala, ta durkusar da tattalin arzikin kasar nan.

Ya kara da cewa:

“A karkashin jagorancin Emefiele, CBN ta gaza a cikin babban aikinta na sarrafa tattalin arziki kuma ta nutse cikin yada farfaganda, tare da ikirarin da ba su nuna mummunan yanayin tattalin arziki da ake fama dashi ba.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here