Jam’iyyar PDP ta Jahar Katsina ta Kori Shuwagabanninta
Jam’iyyar PDP a ƙaramar hukumar Matazu dake jahar Katsina ta kori shugabanta da kuma shugabar mata.
PDP ta yanke wannan hukuncin ne bayan kama su da laifin yin zagon ƙasa ga jam’iyyar a matsayinsu na shuwagabanni.
A cewar shugaban kwamitin riko, an basu damar kare kansu akan tuhumar da aka yi musu amma suka kasa Jam’iyyar PDP ta kori manyan shuwagabannin ta guda biyu a jahar Katsina, waɗanda abun ya shafa sune, shugaban jam’iyyar PDP, da shugabar mata ta jam’iyyar a karamar hukumar Matazu dake jahar ta Kastina.
Read Also:
Shugaban jam’iyyar na riƙon ƙwarya, Alhaji Jabir Adamu, ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa taron masu ruwa da tsaki a PDP wanda ya gudana a ƙaramar hukumar ta Matazu.
“‘Yayan jami’iyyar sun nuna rashin jin daɗin su kan yadda tsohon shugaban da tsohuwar shugabar mata suke gudanar da aikace-aikacen jami’iyyar.” inji Adamu.
“Basu tafiya da kowa ya yin gudanar da ayyukan PDP ɗin. Duk da ambasu dama su bayyana dalilan su na yin haka amma suka ƙi, hakan yasa aka gudanar da zaɓe akan su daga ƙarshe aka kore su.” a cewarsa.
Taron ya samu halartar dukkanin shuwagabannin jam’iyyar harda shi kanshi shugaban da aka kora.