PDP ta Magantu Kan Tafiyar Gwamnan Jahar Ogun, Mataimakiyarsa da Kakakin Majalisar
A halin yanzu, da alama babu kowa a kasa wanda zai yi aiki a matsayin shugaban gwamnatin jahar Ogun.
Wannan ya kasance ne saboda gwamnan jahar, mataimakiyarsa, da kakakin majalisar ba sa Najeriya.
Gwamna Dapo Abiodun da Noimot Salako-Oyedele suna Burtaniya yayin da kakakin majalisar, Olakunle Oluomo, ke Amurka.
Da take Allah wadai da wannan, PDP reshen Ogun ta ce wannan shine babban rashin sanin yakamata a harkokin mulki.
Rashin kasancewar Gwamna Dapo Abiodun, mataimakinsa, Noimot Salako-Oyedele, da kakakin majalisar dokokin Ogun, Olakunle Oluomo, a jahar na haifar da damuwa sosai a jahar.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Abiodun ya bar kasar zuwa Burtaniya don kai ziyarar ban girma ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kwanan nan yayin da Salako-Oyedele ke London.
Bugu da kari, an ce Oluomo yana Amurka don taron kasa da kasa.
Read Also:
Wannan gibi da aka samu a manyan kujeru uku na jahar ya haifar da tsoro, tashin hankali, da zafin martani daga mutane da yawa.
Jaridar ta kuma rahoto cewa a nata bangaren, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana lamarin a matsayin “karshen rashin sanin ya kamata a harkokin mulki.”
Wannan shi ne jawabin shugaban jam’iyyar PDP na Ogun, Sikirulahi Ogundele, wanda ya zanta da manema labarai kan lamarin mai tayar da hankali.
Ogundele ya ce:
“Gwamna ya yi tafiya, mataimakinsa da kakakin majalisa sun bi shi; gaskiya, ban yi takaici ba tunda ba su da alkibla tunda ba su da hangen nesa. Ban ji takaici ba.
“Za a fara bikin ranar ‘yancin kai na shekara-shekara a ranar Juma’a, kawai su koma jahar Ogun su yi bikin ranar.”
Jaridar The Punch ta rawaito cewa anyi hakan ne a wani bangare na kokarin tabbatar da bikin samun ‘yancin kai a ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba cikin nasara.
Legit.ng ta tattaro cewa ginin sakatariyar yana kusa da dandalin Eagles Square kuma cewa za a gudanar da babban taro na ‘yancin kai a ranar Juma’a a wajen.