PDP ta Nada Sabon Mukaddashin Shugabanta

 

FCT, Abuja – Tsagin jam’iyyar PDP a Najeriya ta amince da zaben mukaddashin shugbananta a Abuja.

Jam’iyyar ta zabi Ahmed Mohammed Yayari a matsayin wanda zai jagorance ta na wucin-gadi kafin ɗaukar matakin gaba.

An nada sabon mukaddashin shugaban PDP

Punch ta ce hakan ya biyo bayan dakatar da shugaban PDP, Umar Damagun da aka yi a birnin Tarayya, Abuja a yau Juma’a 11 ga watan Oktoban 2024.

Kafin nadinsa, Ahmed Yayari ya rike mukamin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Gombe, Channels TV ta ruwaito.

Yayari ya rike muƙamin ne daga shekarar 2011 zuwa 2019 a zamanin mulkin tsohon gwamna, Ibrahim Hassan Dankwambo.

An dakatar da wasu jiga-jigan PDP a Najeriya

Da safiyar yau Juma’a 11 ga watan Oktoban 2024, kwamitin gudanarwa karkashin jagorancin Umar Damagun ya dakatar da wasu jiga-jigan PDP.

Yayin zaman, an dakatar da sakataren yada labaran jam’iyyar, Debo Ologunagba da mai ba ta shawara kan shari’a, Kamaldeen Ajibade.

Jim kaɗan bayan daukar matakin, tsagin jam’iyyar ya dakatar shugabannta, Umar Damagun da sakatarenta, Sam Anyanwu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here