Jam’iyyar PDP ce Sanadin Yajin Aikin da ASUU ke yi Yanzu – Festus Keyamo
Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC ya ce jam’iyyar PDP ce sanadin yajin aikin da ASUU ke yi yanzu.
Karamin ministan na kwadago da samar da ayyuka ya ce jam’iyyar PDP ce ta yi yarjejeniyar da ASUU tun shekarar 2019 amma ba ta cika alkawarin ba amma gwamnatin APC na kokarin warware matsalar.
A bangarensa, mai magana da yawun kamfen din dan takarar shugaban kasa na PDP, Daniel Bwala ya ce ita fa jam’iyyar PDP duk lokacin da irin wannan matsalar ya taso tana zaunawa ta tattauna da kungiyoyin kwadago.
Mai magana da yawun kungiyar kamfen din jam’iyyar APC, Festus Keyamo, SAN, ya ce yarjejeniyar da gwamnatin PDP ta yi da ASUU tun shekarar 2019 ne sanadin yajin aiki.
Ka ya bayyana hakan ne hirar da aka yi da shi shirin Daily Politics na Trust TV a ranar Litinin.
Read Also:
Ya kara da cewa tsakanin 1999 zuwa 2015 lokacin da PDP ta mika wa APC mulki, ASUU ta yi yakin aiki sau 12, na tsawon kwanaki 900.
“Wannan lamarin ASUU da ka ke magana. Menene matsalar ASUU yanzu? Yarjejeniyar 2009 ne da gwamnatin PDP ta rattaba hannu. Sun yi yarjejeniya da ASUU da ba su iya cika wa ba. Dole muka yi gadon yarjejeniyar kuma muna kokarin yin sulhu da su.
“Ta yaya gwamnati na kwarai za ta yi yarjejeniya da ASUU kan abubuwan da ba za ta iya cikawa ba wannan shine dalilin da yasa ASUU ke yajin aiki don haka mu fada wa yan Najeriya cewa ASUU na yajin aiki ne saboda yarjejeniyarsu da gwamnatin PDP. Ba APC ne ta yi yarjejeniyar da su ba.
“Ba kaucewa matsalar muke ba; za mu warware matsalar. Daga 1999 zuwa 2015 lokacin da suka mika wa APC mulki, ASUU ta je yajin aiki sau 12. Ina da alkalluman ya kai kwana 900.”
Amma da ya ke martani, mai magana da yawun kamfen din dan takarar shugaban kasa na PDP, Daniel Bwala, wanda shima ya bayyana a shirin tare da Keyamo, ya ce a lokacin da ASUU ko wata kungiyar kwadago suka tafi yajin aiki, a kan rika tattaunawa mai amfani tsakanin bangarorin biyu.