Masu Faɗa a ji a Jam’iyyar PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC

 

Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Kebbi sun sauya sheka, sun kama tsintsiyar jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Jiga-jigan sun koka da irin rikicin cikin gida da jam’iyyar PDP ta fuskanta yayin da ake ci gaba da shirin 2023.

A kwanakin baya ne ake ta kai ruwa rana tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP da gwamna Wike na jihar Ribas.

Zuru, jihar Kebbi – Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP hudu a masarautar Zuru ta jihar Kebbi tare da magoya bayansu sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, rahoton Daily Sun.

Wadannan jiga-jigai da suka sauya sheka sun hada da Alhaji Shehu Ribah daga Danko/Wasagu; Alhaji Nuhu Goma daga Zuru; Alhaji Adamu Jalalo daga Fakai da Alhaji Babuga Diri daga kananan hukumomin Sakaba na jihar.

Manyan jiga-jigan jam’iyyar APC karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Alhaji Samaila Yombe-Dabai, da shugaban jam’iyya a jihar, Alhaji Abubakar Kana-Zuru ne suka tarbe su a wani taro da aka yi a Zuru ranar Lahadi, PM News ta ruwaito.

Da yake karbar wadanda suka sauya shekan, Yombe-Dabai, wanda ya taya su murnar shiga jam’iyyar APC, ya bayyana taron a matsayin wani gagarumin ci gaban siyasa a jihar.

Ya kuma tabbatar wa wadanda suka sauya shekan cewa za su hada kai a dukkan al’amuran jam’iyyar APC a matsayin ‘ya’yan jam’iyyar na gaskiya.

Gwamnan Kebbi ya gina al’ummar jihar, inji mataimakin gwamna

A cewar mataimakin gwamnan jihar:

“Muna yabawa Gwamna Atiku Bagudu bisa tabbatar da gina al’ummar jihar. Irin wannan karimcin daga gare shi ne ya sa jama’a suke ta tururuwa zuwa jam’iyyar.”

Hakazalika, Kana-Zuru ya taya wadanda suka sauya sheka murnar shiga jam’iyyar APC, inda ya ce mataki ne da ya dace. A cewarsa, sabbin mambobin za su samu daidaito da adalci da karramawa a cikin jam’iyyar.

A nasu jawabin, jiga-jigan hudu sabbin shiga APC sun danganta matakin ficewa daga jam’iyyar PDP da rikicin da ke cikinta.

Wasu daga cikin muhimman mutanen da suka halarci taron sun hada da Alhaji Abubakar Nayaya, shugaban hukumar ma’aikata ta karamar hukumar; Alhaji Kabiru Tukura, dan majalisar wakilai.

Wasu kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman ga gwamna su ma sun halarci taron.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here