Jiga-Jigan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Kebbi
Rahoton da muke samu daga jihar Kebbi na bayyana cewa, wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC.
Jam’iyyar APC a jihar ta karbe su, ta kuma ba su damar fadin abubuwan da ya ja suka bar jam’iyyar PDP ta adawa.
Ana ci gaba da bikin sauya sheka yayin da ake ci gaba da jiran zaben 2023 mai zuwa nan ba da jimawa ba.
Jihar Kebbi – Jam’iyyar APC a jihar Kebbi ya karbi wasu jiga-jigan siyasan da suka sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP, PM News ta ruwaito.
Daya daga jiga-jigan da suka sauya sheka akwai tsohon babban oditan PDP, Alhaji Rabi’u Sa’idu, tsohon sakateren kwamitin riko na PDP Alhaji Sirajo Ibrahim da wasu manyan mambobin PDP 15 daga unguwar Bubuce a karamar hukumar Augie ta jihar.
Read Also:
Sauran sun hada da Umaru Wakkala, mataimakin shugaban PDP na Bubuce; Salihu Shayi, shugaba matasan yankin; Alhaji Idi Babuce, ma’ajin jam’iyya da kuma Hamza Akilu, oditan jam’iyya.
Dalilin komarsu APC Jim kadan bayan bayyana shiga APC, tsohon babban oditan, ya yaba da irin ayyukan da gwamna Atiku Bagudu ke gudanarwa a jihar.
Ya kuma ce, ya fice daga PDP ne saboda rashin adalci da kuma tauye musu hakki da ake yawan yi a jam’iyyar, rahoton Punch.
Sa’idu ya kuma yabawa Magajin Rafin Kabı da Alhaji Bello Dantani a kokarinsu na ganin sun daura shi a turbar shiga jam’iyyar APC tare da mabiyansa.
Shi kuwa Augie cewa ta yi:
“Na yaba da aikin titin da aka yi a karamar hukumar Augie a karkashin mulkin sanata Abubakar Atiku Bagudu.
“Wannan hanyan da aka yi a karkashin mulkin sanata Abubakar Atiku Bagudu na daya daga cikin masu muhimmanci.”
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban APC na karamar hukumar, Alhaji Bashir Isah-Mera; Lawal Muhammad-Yola, shugaban karamar hukumar Augie; Alhaji Haruna Maitandu, shugaban hukumar jin dadin alhazzai, da tsohon daraktan ma’aikatar kwadago, Alhaji Bello Dantani.