PDP: An Tashi Taron Jam’iyyar Lafiya Babu Saɓani

 

Taron jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya da gabaninsa aka dauka za a tashi baran-daran ko kuma a yi ta kare tsakanin ‘yan arewa da kudu, sai ga shi an shiga daki an rufe kofa an yi shi kalau.

Abin da aka yi tsammani za a samu ƙiƙi-ƙaƙa da rarrabuwar kawuna a taron kwamitin zartarwar PDP a jiya shi ne shugabancin jam’iyyar sai dai hakan bai yiwu ba.

Hakan ya faru ne kasancewar jam’iyyar ta amince da warewa bangaren arewaci shugabancin PDP ɗin, amma kowanne yanki na da damar fitowa a dama da shi a takarar shugabancin kasa.

Felix Hassan shugaban PDP na jahar Kaduna kuma shugaban kungiyar shugabanin jam’iyyar PDP na jahohi, ya ce abin da ya faru ba sabon abu ba ne, kuma a cewarsa ganin yadda ‘ya’yan jam’iyyar suka tashi suna haba-haba da juna to sun dauki turbar dinke barakar da ke neman yi musu sakiyar da ba ruwa.

Shugabancin PDPn  dai ya nanata cewa matakin rarraba mukaman bai shafi shugabancin kasa ko na majalisa ba.

A karshen wannan watan ne jam`iyyar PDP za ta yi babban taron ta na kasa, inda magoya bayan ta za su zabi sababbin shugabanni.

Tun da farko dai a kalamansa gabanin fara taron kwamitin zartarwar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce matakin da PDP ta dauka kan yankin da zai fitar da dan takara da sauran batutuwa su ne za su yanke hukunci kan zaben 2023.

Wasu na kalloon kalaman a matsayin ba-girin-girin-ba ta yi mai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here