Peter Obi ya Ziyarci Gwamna Wike a Port Harcourt
Gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa, ana ci gaba da tattaunawa a tsakanin manyan yan siyasa.
Hotunan Peter Obi yayin da ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike sun haddasa cece-kuce a bangaren siyasar kasar.
Ana ta rade-radin cewa Wike ya fusata kan hukuncin da Atiku Abubakar na yanke na kin daukarsa a matsayin abokin takararsa gabannin zaben mai zuwa.
Rivers – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, ya ziyarci gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a Port Harcourt a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni.
Read Also:
Legit.ng ta tattaro cewa sun shafe tsawon awanni suna saka labule a tsakaninsu a gidan Gwamna Wike da ke Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.
Ana dai ta rade-radin cewa Wike na shirin ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP bayan ya fadi a zaben fidda gwanin jam’iyyar sannan kuma aka ki zabarsa a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar, wanda zai daga tutar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.
Tuni hotunan ganawar tasu suka karade shafukan soshiyal midimiya musamman ma a kan Twitter.
Haduwar manyan yan siyasar biyu ya haddasa cece kuce kasancewar yanzu ba a ga maciji tsakanin Wike da wasu mambobin jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP).