Dokar Kulle: Mazauna Jahar Plateau Sun Koka da Karancin Abinci
Al’umman garin Jos da ke jahar Filato sun koka a kan dokar kulle na sa’o’i 24 da gwamnatin jahar ta sanya.
Sun bayyana cewa hakan ya kawo karancin abinci da kuma tsadar kayayyakin amfani na yau da kullun.
Don haka sun roki gwamnatin da ta sassauta tare da tura jami’an tsaro zuwa yankunan da ake tashin hankali.
Filato – Mazauna garin Jos, a ranar Asabar, 28 ga watan Agusta, sun koka kan karancin kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki a yankunansu bayan sake sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a yankin.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mazauna yankin sun kuma koka game da hauhawar farashin kayan abinci bayan umarnin.
Gwamnatin jahar ta sake sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 bayan kisan wasu ‘yan kabilar Anaguta a ranar Talata a unguwar Yelwa Zangam da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.
Jaridar ta kuma rahoto cewa mazauna yankin da suka fito neman abinci sun koka game da halin da ake ciki.
Read Also:
Yakubu Busari, wani mazaunin Janta Adamu, ya ce mutanen yankin na fuskantar wahalar gaske don shawo kan lamarin, yana mai cewa dokar hana fita duk da cewa tana da mahimmanci, ta haifar da wahalhalu a yankin.
Ya ce:
“Samun abincin ya zama matsala. Mutane da yawa ba su da kuɗi saboda dole ne su fita kafin su sami wasu kuɗi don siyan abinci.
“Ba a samun katin waya saboda shaguna da yawa ba sa aiki.
“Halin na iya haifar da sata da sauran miyagun ayyukan a cikin al’umma.”
Peter Azi, wani mazaunin Laminga, ya ce:
“Dokar hana fita na shafar mazauna yankin na mu ta kowane fanni na rayuwarsu.
“Mutane ba sa iya zuwa cikin gari don samun damar kula da lafiyarsu.
“Kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki sun yi karanci sosai saboda masu siyar da kayan galibi suna zuwa garin don kawo masu kayayyaki yanzu kuma garin yana kulle.”
Hamza Musa, wani mazaunin Anguwan Rogo, ya ce:
“A ganina, ya kamata gwamnati ta sassauta dokar hana fita. Mutane suna fama da yunwa kuma yakamata a kyale su fita su samo abinci su ci.
“Lokacin da yunwa ta zama ba za a iya jurewa ba kuma mutane sun yanke shawarar fita, gwamnati na iya hana mutane.”
A yayin da suke kira da a dage dokar hana fita, mazauna garin da dama sun bukaci gwamnati da ta tura jami’an tsaro a duk wuraren tashin hankali don kare rayuka da dukiyoyi.