Gwamnan Jahar Plateau ya Magantu Kan Kashe Matafiya 25

Gwamnan Jahar Plateau Simon Lalong, yayi Allah wadai tare da nuna bakin ciki, akan harin da aka kaiwa matafiya a ranar Asabar, akan hanyar Rukuba dake Karamar Hukumar Jos ta Arewa, inda aka kashe mutane da dama.

Gwamnan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daraktan Yan Jarida da Harkokin Al’umma Makut Macham ya fitar a Jos.

Gwamnan Jahar Plateau
Ya bayyana cewa Gwamnatin Jahar Plateau bazata lamunci kisan mutanen ba gaira ba dalili, inda yace za’a dauki mummunan Mataki ga Wadanda suka dauki nauyin kisan, domin ya zama izna ga saura.

Lalong ya gargadi masu son tada zanne tsaye a Jahar Plateau, dasu daina, domin gwamnti bazata lamunci rashin bin doka, wanda ka iya ruguza zaman lafiyar Jahar.

Gwamnan ya kara dacewa, an tura jami’an tsaro domin maido da zaman lafiya a yankin, tare da ganowa gami da kama wadanda suka aikata laifin.

Ya yabawa Hukumomin tsaro na kai daukin gaggawa, wanda ya bada nasarar kama wasu daga cikin wadanda ake zargin, da Kuma maido da kwanciyar hankali a yankin.

Ya bada tabbacin kiyaye rayukan Yan kasa, a sa’ilinda tuni jami’an tsaro aka turasu a yankin, da Kuma gaba dayan Birnin Jahar, domin magance sake afkuwar wannan mummunan lamari.

Ya bukaci Yan Jahar dasu zama masu hakuri, gami da kawo rahoton duk wani Wanda ake zargi a yankunan su ga Jami’an tsaro, domin daukar matakin gaggawa.

Gwamnan ya kuma umarci Sakataren Gwamnatin Jahar Danladi Abok-Atu daya ziyarci yankin domin gano yanayin lamarin, tare da tabbatar da cewa an kula da wadanda suka ji raunuka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here