Hana Fita: Gwamnatin Jahar Plateau ta Sassauta Dokar Tare da Janye Dokar Hana Tuka Keke NAPEP

 

Gwamnatin Filato ta janye dokar hana tuka Keke NAPEP a garin Jos da kewaye tare da sassauta dokar hana zirga-zirga, a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

Gwamnan Jahar, Simon Lalong, ne ya amince da hakan bayan kammala taron Majalisar Tsaron Jahar.

A yanzu dokar hana zirga-zirga ta dawo daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe.

Filato – Gwamnatin jahar Filato ta sanar da sake sassauta dokar hana fita a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Dakta Makut Macham ya fitar, ya bayyana cewa gwamnati ta kuma dage haramcin da aka sanya a baya a kan tuka adaidaita sahu a jahar.

Macham ya bayyana cewa gwamnan ya amince da hakan ne a ranar Talata bayan taron kwamitin tsaro na jahar da aka gudanar a sabon gidan gwamnati a Jos, Aminiya ta rawaito.

Sanarwar ta ce:

“Daga ranar Laraba, 8 ga Satumba 2021, dokar hana fita a Jos ta Arewa za ta fara aiki daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

“Wannan zai yi daidai da matsayin dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta Kudu da Bassa wanda har yanzu yana daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

“Hakanan, Gwamna Lalong ya kuma amince da cewa daga ranar Laraba, 8 ga Satumba 2021, za a dage dokar hana zirga -zirgar adaidaita sahu daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a kullum. Wannan yana nufin cewa ba za a bar wani adaidaita ya yi aiki tsakanin awanni 6 na yamma zuwa 6 na safe ba.”

Sai dai gwamnan, ya bayyana cewa haramcin babura a cikin garin Jos/Bukuru zai ci gaba da aiki, yana mai cewa za a ci gaba da tabbatar da ganin an kama masu laifin da kuma hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Gwamnan ya yabawa al’umman jahar kan haɗin kai da fahimtar da suka nuna a lokacin hare-haren da kuma dokar hana fita.

Ya bukace su da su ci gaba da marawa gwamnati baya don dawo da zaman lafiya a fadin jahar, Channels TV ta rawaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here