‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Banga 5 a Hanyar Birnin Gwari Dake Jahar Kaduna

 

‘Yan bindiga sun kai wa wasu ‘yan banga farmaki inda suka kashe mutum biyar a hanyar Birnin Gwari da ke jahar Kaduna.

Lamarin ya afku ne a ranar Talata, 7 ga watan Satumba, a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga Kaduna.

Zuwa yanzu ba a ji ta bakin rundunar ‘yan sandan jahar ba.

Wasu ‘yan bindiga sun halaka ‘yan banga biyar sakamakon bude masu wuta da suka yi a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa wani jigo a yankin, Liman Hussaini Udawa, ya tabbatar da harin inda yace an kai wa yan bangar harin ne a kusa da unguwar Yako da ke hanyar.

Ya kara da cewa yan bangar na a hanyarsu ta dawowa daga Kaduna ne lokacin da lamarin ya afku.

Ya ce:

“Maharan sun yi masu kwanton bauna inda suka kona motarsu a kusa da unguwar Yako a kan babbar hanyar. A yanzu haka mun dauko gawarwakin ‘yan bangar su uku.”

Ya kuma bayyana cewa za a binne su a garin Udawa da ke karamar hukumar Chikun ya jahar Kaduna.

Wasu majiyoyi a yankin sun ce an kai wa yan bangar harin ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Talata.

Sai dai jaridar ta kuma ruwaito cewa babu wani jawabi daga Kakakin yan sandan jahar, ASP Jalige Mohammed, domin bai amsa kiran waya da sakon tes da aka aika masa ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here