‘Yan Fashin Daji da Aka Kora Daga Jahar Zamfara Sun Kai Hari Sokoto

 

Rahotanni daga Sokoto da ke arewacin Najeriya sun ce wasu mahara da ake zaton ƴan fashin dajin da jami’an tsaro suke yi wa luguden wuta ne a dazukan jahar Zamfara na kwarara cikin wasu yankunan jahar.

Wasu mazauna yankin ƙaramar hukumar Dange-Shuni sun shaida wa BBC cewa maharan sun shiga ƙauyuka da dama na yankin inda suka yi awon gaba da kusan mutum 20.

Gwamnatin jahar Sokoto ta bayyana cewa tun bayan da gwamnatin jahar Zamfara ta fara ɗaukar matakai a kan ƴan fashin dajin, ita ma ta ƙarfafa tsaro a iyakokinta.

Mazauna yankin sun ce cikin kwanaki biyu da suka gabata ƴan bindigar sun kai hare-hare da tsakar dare, inda suka sace mutane da dama a ƙauyukan yankunan Dange-Shuni da Illela.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ana kyautata zaton cewa ƴan bindigar sun fito daga maƙwabciyar jahar Zamfara ne.

A cewarsa: ” ‘Yan bindigar sun shiga wani gari da ake kira Fajanbi inda suka yi awon gaba da mutum tara.

“Maharan sun tafi da mutum guda a wani ƙauye wanda daga bisani ya kubuta, amma bayan dawowarsa mutumin ya ce sun kai su ashirin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.”

A gefe guda, mahukuntan Jahar Sokoto sun ce tabbas akwai ƴan fashin daji da kan tsallaka daga jahar Zamfara domin su tafka ta’asa amma ba kamar yadda aka bayyana cewa suna kwasar mutane ba.

Sai dai sun ce tun bayan da gwamnatin jahar Zamfara ta fara ɗaukar matakai a kan ƴan fashin dajin a yankunanta, su ma suka ƙarfafa tsaro a iyakokin jahar.

A cewar Kwamishinan Tsaro na jahar Sokoto, Kanal Garba Moyi, sun ɗauki matakan daƙile ƴan fashin da aka kora daga jahar Zamfara.

Sai dai duk da haka wasu na ganin cewa akwai bukatar ganin cewa gwamnatin jahar Sokoto ta ƙara duba sauran kafofin da mai yiwuwa ta nan ne waɗannan ƴan bindiga da ke tserewa daga jahar ta Zamfara ke shiga Sokoto.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here