Ambaliyar Ruwa a Jigawa: Gidauniyar Ƙasar Qatar da ta Malam Inuwa Sun Raba Tallafin Abinci ga Mutane 1,000

Biyo bayan iftila’in ambaliyar ruwa da ta afkawa al’ummar Jihar Jigawa a bara, gidauniyar ba da agaji ta Duniya, (Qatar Charity Foundation) da haɗin gwiwar (Gidauniyar Malam Inuwa) ta mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, (CCIE), sun raba tallafin kayan abinci ga mutane (1,000) daga cikin mutanen da iftila’in ambaliyar ta shafa.

Rabon kayan wanda aka ƙaddamar da shi yau a ofishin gidauniyar da ke kan titin Garun-Gabas, a ƙaramar hukumar Haɗejia, an rabawa mutane (600) nasu waɗanda aka zaƙulo daga ƙananan hukumomi takwas da ke yanƙin ƙasar Haɗejia inda daga bisani za a rabawa sauran yankunan.

Da ya ke bayani jim kaɗan bayan kammala rabon, shugaban gidauniyar Malam Inuwa, Dakta Hussaini Yusuf Baban ya bayyana cewa an warewa yankin ƙasar Haɗejia kason mutum ɗari shida ne duba da girman annobar a yankin.

Da ya ke tsokaci dangane da hanyoyin da su ka bi wajen zaƙulowa gami da tantance mutanen da su ka amfana da tallafin kuwa, Dakta Baban ya bayyana cewa: “Mun tuntuɓi shugabannin ƙananan hukumomi haɗi da Limamai da kuma amintattun mutane wajen haɗa sunayen. Kuma duk wanda mu ka ba wa wannan tallafi ɗaya ne daga cikin mutanen da ruwa ya yi wa ɓarna in ma a gida ko a gona,”. Inji shugaban gidauniyar.

Kayayyakin da aka raba ɗin sun haɗa da: Taliya, Shinkafa, Semovita, wake da Mai. Mutanen da su ka amfanan sun yi godiya haɗi da addu’ar fatan alkhairi ga gidauniyoyin biyu bisa tallafin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here