Wasu Jihohin Sun Fara Raba wa Talakawa Tallafin Korona

Bayan bata-gari sun fara balle ma’adanar kayayyakin tallafin COVID-19 cikin kwanakin da suka gabata, suna kwashe kayan abinci

Cikin gaggawa gwamnonin jihohi sun fara raba kayan tallafi ba tare da jiran umarnin gwamnatin tarayya ba – Duk da dai har yanzu ba’aji komai ba daga bakin shugaban kasa ko kuma ma’aikatar jin kai da walwalar ‘yan kasa ba Cikin gaggawa gwamnonin jihohi 36 da ke Najeriya da babban birnin tarayya Abuja sun fara rarraba kayan abincin tallafin COVID-19, ba tare da jiran umarnin gwamnatin tarayya ba. Tun ranar Larabar da ta gabata ne bata-gari suka fara balle ma’adanar kayayyakin tallafin COVID-19 na jihohi suna kwashe kayayyakin abinci da sunan zanga-zangar EndSARS. A cikin kwanakin da suka gabata ne jihohi suka yi ta bayar da dalilan da suka hana su raba kayan tallafin tuntuni, Daily Trust ta wallafa.
Duk da har yanzu ba a ji komai ba daga bakin shugaban kasa da ma’aikatar jinkai da walwalar ‘yan kasa ba, a kan ko sun san cewa gwamnatin jihohi basu raba kayan tallafin ba. Dama mutane da dama sun yi ta caccakar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin APC akan kayan tallafin da sukace sun bayar a raba wa ‘yan Najeriya. Ba Buhari  kadai ba, hatta ministan tallafin da jin kai ba a barta ta huta ba da kalubale.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here