Zamfara: ‘yan Bindiga Sun Saci Hakimi da Mutune a ƙauyen Lingyaɗo

Jama’a sun watse daga ƙauyen Lingyaɗo na ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, sakamakon wani hari da ‘yan bindiga suka kai masu, suka yi awon gaba da mutum fiye da 50 ciki har da hikimin garin.

Sai dai rundunar ƴan sanda jihar ta ce duk da cewa an kai harin, to mutum biyar kawai aka sace ciki har da hakimin garin.

A yanzu haka jama’ar garin Lingyaɗo sun warwatsu a garuruwa daban-daban inda suke samun mafaka, sakamakon yadda ƴan bindiga suka hana su sakat da yawan hare-hare.

Wani mutum ɗan garin Lingyaɗo da yanzu haka yake gudun hijira a wani garin daban, ya shaida wa BBC yadda maharan suka yi wa ƙauyen nasu dirar mikiya.

”Kawai sai ga su kwatsam da baburwa, babu ma san yawan baburan ba amma dai suna da yawa. Kowanne babur da mutum uku a akai kuma ko wannensu na ɗauke da bindigarsa.

“Sai da suka zagaye garin sannan suk dinga harba bindigar sama, da zarar mutum ya fita sai su tare shi. Da haka har suka tara mutane da yawa suka tafi da su, ciki har da hakimin garin namu.”

Ya kara da cewa: ”Sun tafi da kusan mutum 50 da ƴan kai, yawancinsu maza ne sai yara kaɗan. Dama matan garin duk sun daɗe da watsewa saboda rashin arziƙin da suke zuwa suna yi musu akai-akai.

“Ba a kwana biyu dama sai sun zo sun yi wa matanmu wulaƙanci irin yadda suke so sannan su tafi, to sai garin ya dawo daga maza kawai sai ƴan yara,” in ji mutumin.

Kwana a daji
Wannan hari dai ba shi ne na farko da aka taɓa kai wa Lingyaɗo ba, ”ko yaushe suna kawo mana hari saboda ba mu da jami’an tsaro a nan garin, tun daga kusan shekara uku da ta wuce ba mu da jami’an tsaro, kuma mun manta rabon da mu ji daɗin garinmu don yawanci a daji muke tafiya mu kwana,” in ji mutumin.

Mutumin ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka ta aike musu da jami’an tsaro yankin nasu.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya ta jihar Zamfara SP Muhammed Shehu ya shaida wa BBC cewa yawan mutanen da aka sace ɗin bai kai 50 ba.

”Bayanan da muke da su wanda DPO na wannan yankin ya ba mu, su maharan sun samu damar yin awon gaba da maigarin ne da wasu mutum huɗu kawai, ka ga mutum biyar kenan.

”Ba su samu damar tafiya da sauran mutanen da suka tattara ɗin ba, duk sun watse sun tsira. Amma duk da haka kwamishinan ƴan sandan jihar Zamfara ya tura jami’an tsaro yankin don bin sawun maharan don a kuɓutar da waɗanda suka sace tare da kama maharan,” in ji shi.

Me ake yi don kai tsaro yankin?
Ganin cewa mutanen garin sun koka cewa an shafe lokaci mai tsawo ana kai musu hare-hare, BBC ta tambayi ƴan sanda ko akwai matakin da aka ɗauka don kai tsaro wajen?

Sai mai magana da yawun rundunar ya ce kamar yadda aka ɗauki matakin kai jami’an tsaro na haɗin gwiwa yankuna daban-daban, ”shi ma wannan garin ana ɗaukar irin wannan matakin na tabbatar da cewa an kai jami’an tsaro da za su magance irin wannan lamarin.”

Matsalar tsaro na ci gaba da zzma gagrumin ƙalubale a jihar Zamfara da wasu jihohin da ke maƙwabtaka da ita da ma yankin arewao maso yamma da arewao maso gabashin ƙasar baki ɗaya, al’amarin da ke buƙatar sake tashi tsaye don magance shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here