Daga Huzaifa Dokaji

Tarihi shine jigon dukkan wata al’umma. Babban burin dukkan al’ummar da ta san knata shine gina tare da kare tarihinta. Kasashe da dauloli da dama, kamar Kasar Sin da Daular Farisa sun yi shura kwarai wajen riko tare da dabbaka al’adunsu.
Kasar Kano kasace da ta shahara a fadin duniya. Kano ta yi fice saboda dimbin tarihin da masarautarta ta kafu a kai. Kusan ma iya cewa babu wani gari a kasar Hausa ko ma a Afirka ta Yamma da ya ja hankalin ko da Turawan Mulkin Mallaka irin Kano. Ra’ayin irin wadannan Turawa da daman na kara nuni da hakan. Misali, Lugard ya taba fadar cewa tunda yake, bai taba tunanin a Afrika za a samu wani abu da zai hankalinsa ya burgeshi ba irin badalar Kano. Robinson ya siffanta Kano a matsayin Landan din kasasehen bakar fata. Babban abinda ya kai Kano wannan matsayi shine tsari da fasalin masarautar da ke mulkin ta.
Tarihin Kano ya kafu ne akan Sarauta. An fara sarauta a Kano kimanin shekaru dubu da suka shude. Tsahon wannan Shekaru, zuri’ar mutum biyu ne kawai suka mulki Kano in ban da dan takin da Sarki Sulaimanu dan Aba Hamma (1807-1819) yayi mulki bayan Fulanin Jihadi sun ci Kano da yake. Duk da sauya-sauyen da Jihadi ya kawo a tsarin rayuwar mazauna kasar Hausa, Jihadin bai samu damar sauya tsarin sarautar Kano ba. Ma iya cewa, maimakon ma Jihadi ya ci sarautar Kano da yaki, Sarauatr Kano ce ta ci masu Jihadin da yakin al’ada.
Zuwan Turawan mulkin mallaka ba chanja wannan tsari na kusan karni 8 ba. Turawa sun bar al’ada yanda suka tarar da ita. Ko da yake an kirkiri gundumomi guda 24 a shekarar 1906 saboda gyara harkar karbar haraji, sai dai fasalin gundumomin bai saba da ainihin tsarin mulki na kasar Hausa ba. Wannan tsari, ko da gwamnatin Alhaji Abubakar Rimi da ta zo, duk da ta raba masarautar ta hanyar daga darajar sarakunan yanka zuwa daraja daya da Sarkin Kano, sai dai ba ta ci zarafin tsarin gunduma ba. Kowanne sarki an bashi iya abinda tarihin kasarsa ya mallaka masa ne. Rimi bai kirkiri wata sabuwar masarauta da babu ita a jiyan Kano ba.
Matakin da Sardauna ya dauka ne tsige Sarakunan da aikinsu ya saba da abinda gwamnatinsa take sa rai, ya nuna cewa bakar fata ma na da karfi da dama cire rigar Sarakunan a sabuwar tafiar yancin kai da aka dauko. Bugu da kari, cire Sarkin Musulmi da Janar Babangida da Janar Abacha su ka yi, ya nuna cewa babu wani Sarki da zai tsira daga siyasar mulkin zamani. Matakin da Rimi ya dauka na sauya fasalin matsayin wasu daga cikin sarakunan yanka da ke cikin yankin tsohuwar Jihar Kano ya kara bude wata kofa a tarihin Kano wadda ko Sardauna bai bude ta ba. Matakin na Rimi ya daga martabar Sarakunan Gaya, Rano dss zuwa daraja daya da ta Sarkin Kano. Hakan ya nuna cewa ba wai iya Sarkin Kano ba, a’a, masu mulki na da damar yiwa al’adar Kano hawan kawara matukar hakan zai biya bukatarsu ta siyasa. Hakan ya jawo rudu kwarai musamman ganin cewa ko da Turawan mulkin mallaka na taka tsantsan wajen aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi harkar gargajiyar Kano.
Wannan yunkuri na Gwamna Rimi ya fuskanci tawaye daga mutane da dama a ciki harda malaminsa na siyasa wato Malam Aminu Kano. Kamar yadda Alan Feinstein ya rawaito a littafinsa na African Revolutionary, Malam ya siffanta aikin na Rimi da ‘tabin hankali’ ko kuma “zauta”. Duk da akan tarbiyar Malam din Rimi ya tashi tare da kuma gina hujjarsa ta yiwa masarautar ta Kano fyadar ‘ya’yan kadanya, Malam din ne ya bada shawara mafi girma ta yanda za a bata wannan yunkuri na Limamin Chanji.
Tashin hankalin da ya biyo bayan wannan abu da Rimi yayi, ya dakushe yunkurin yan siyasa da suka biyo baya na daukan matakai tsaurara akan sarakunan gargajiya ko da akwai bukatar hakan. A bangaren Sarakunan kuma, hakan ya zama izna na su kame bakunansu daga al’amuran siyasa. Wannan ka iya zama dalilin da yasa mutane da dama a Arewa ke kallon Sarakunan a matsayin mutanen da ba sa kishin al’ummarsu. An dinga nunen yatsa akan cewa Sarakuna jemagu ne, masu goyawa mai mulkin da ke da dama, wanda hakan ya saba da tarbiyyar magabatnsu da su kai ta fama da Turawa akan abinda ya kamata da wanda bai kamata ba. Idan mu ka dawo Kano, kame kai daga tsoma baki a harkar yan siyasa bata hana tangarda tsakanin Sarki Ado da gwamnonin da suka biyo bayan Rimi ba. Wasu an sani, wasu kuma a boye suka faru. Kame bakin da Sarkin ya yi na tsahon lokaci ya zama al’adar Sarakuna da dama har wasu na ganin hakan shi ne abinda ya kamaci masu mulkin gargajiya.
Sai dai shirun na Mai Garin Birni ya kuma samun sauyi a lokacin da Malam Ibrahim Shekarau ya hau mulki. Tsananin biyayyar da Shekarau ya nuna masa, ta kai ga har marigayin ya yi masa sarautar Sardaunan Kano, kuma ya nada shi dan majalisarsa. Kalaman Sarkin ga dan takarar da Sardaunan ya tsayar, wato Mal Salihu Sagir Takai, sa’ilin da ya kai masa ziyarar neman albarka, sun kara kafa tushen fadada rashin fahimta tsakanin marigayin da Kwankwaso. An buga tataburza ainun wanda ba dan shiga tsakani da manyan mutane irinsu Marigayi Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim su ka yi ba, da ba a san iya abinda rikicin zai zama ba.
Yau ma dai, ga mu cikn wani rikicin tsakanin sabon sarki da gwamnatin Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Shin wannan takaddama ta Sarki da gwamnan ta na da kamanceceniya da waanda suka gabaceta? Ma iya cewa akwai alaka saboda abu biyu. Da farko dai, dukkan gwamnonin da suka samu tsattsamar alaka da masarautar ta Kano almajiran Malam Aminu Kano ne. Na biyu, dukkansu ‘ya’yan dagatai ne. Watakila hakan ne ma ta su wasu ke ganin rigimar ba wani abu bace face tsohuwar rigimar nan ta tsakanin ‘ya’yan dagatai da ‘ya’yan hakimai ko Sarakuna.
Shin yunkurin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na raba masarautar ta Kano shi ma tasiri ne na wadannan abubuwa guda biyu da aka fada a baya? Ko kuma da gaske ya yi hakan ne domin ci gaban al’umman yankunan da abin ya shafa? Amsar wadannan tambayoyi na da alaka kwarai da juna. Lallai akwai raba hanya tsakanin manufar Gwamnatin Rimi, Kwankwaso da ta Ganduje. Sa’ilin da ya zama gwamnatin Rimi ta nuna damuwarta kwarai da bukatar ‘ya’yan talakawa, wannan gwamnati ba ta da alaka mai karfi da irin wannan manufa. Idan kuwa haka ne, akwai alamar tambaya kwarai akan kyawun niyyarta a wannan yunkuri musamman duba da hangar da ta bi domin cimma manufar ta ta raba masarautar ta Kano. Idan muka dora rikicin a mizanin na Kwankwaso da Sarki Ado, za mu ga cewa suna kama da juna ta fuskar dalili. Duka rikicin guda biyu sun faru ne akan zargin gwamnonin na cewa Sarakunan basu basu goyon baya ba a wajenmatasa. Idan kuwa har hakane, akwai bukatar mu duba dalilan sarakunan.
Kididdigar masana a fadin Najeriya ta nuna cewa babu jihar da ta kai Kano yawan almajirai da matasa marasa ilimi da aikin yi. Sanin kanmu ne cewa kaso mafi tsoka na wadannan matasa sun fito ne daga bangare da Mai Girma Gwamna yake kokarin kafa sabbin masarautu. Akwai bukatar a duba cewa wadannan yankuna sun fi bukatar ilimi, aikin yi da tsaro akan masarautu. A wannan yanayi na tsitsistsi da kowacce kasa ke kokarin rage kudaden da take kashewa na gudanarwa, babu hikima gwamanatin da ba ta iya rike masarauta daya da kyau ba, tace zata kara har wasu guda hudu. Akwai siyasa kwarai idan aka duba cewa gwamnnati ba ta yi la’akari da wadannan abubuwa ba kafin ta kara masarautun. Domin kudaden da za a kashe wajen gina gidajen sarautun da sarakunan da hakimansu za su zauna, da albashin da za a dinga biyansu da motocin hawan da za a siyawa kowannensu sun isa a kaddamar da ayyukan ci gaban al’umman wadannan yankunan.
Akwai bukatar jama’a su yiwa wannan abu karatun ta nutsu ta hanyar neman gamsassun bayanai daga wakilan da suka zartar da wannan ta’asa. Misali, me yasa zartar da wannan doka ya yi daidai da zartar da dokar albashin dindin ga shugabancin majalisar ta Kano? Shin akwai alaka tsakanin burin shugaban majalisar na Kano na zama ‘kingmaker’a masarautarsa ta Rano da yake rike da sarautar Turakin Rano musamman duba da cewa dokar ta shigar da mai rike da wanan sarauta, kamar yadda wata jarida ta rawaitar a rahotonta na musamman akan rikicin? Shin akwai alfanu gwamnatin da bata iya samar da kudin shiga na a zo a gani ta kara sabautar da asusun jihar Kano saboda bukatarta ta kirkirar masarautu da kuma biyan kudin kwalliya ga wadanda suka tayata tabbatar da wannan kudiri? Yanzu shikenan an yi amfani da karfin mulki an murde zabin mutanen Kano, amman duk bai isa ba, kuma sai an kara bin tarihi da al’adarsu an musu dukan kawo wuka? Shin ina laifin sarki idan yace mutane su zabi shugabanni na gari, wadanda za su kare mutuncin Kano da mutanenta? Ko dai biri ya yi kama da mutun ne, shi ya sa mai suna ya amsa sunansa?

The post Raba Masarautar Kano: Akwai lauje cikin nadi appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here